
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya halarci ɗaurin auren Halima Junaid, wadda jikar marigayi tsohon shugaba Muhammadu Buhari ce da angonta Walid Mu’azu, wato ɗan Iyan Katagum.
An gudanar da ɗaurin auren ne a masallacin Juma’a na Yahaya Road da ke Unguwar Rimi a Birnin Kaduna.
Daga cikin waɗanda suka raka Mataimakin Shugaban ƙasar akwai; mataimakin shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia; Ministan Muhalli, Alhaji Balarabe Lawal; Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali; da Ɗan majalisa Lawal Zannah.
Haka kuma Shettima shi ne wanda ya bada auren amaryar yayin da Alhaji Shehu Mu’azu ya karɓa a madadin angon.
Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da tsohon Antoni Janar na Ƙasa kumq Ministan Shari’a Abubakar Malami SAN; tsohon shugaban EFCC, Abdulraseed Bawa; Yusuf Muhammadu Buhari; tsohon Darakta-Janar na hukumar SSS, Malam Yusuf Bichi da Alhaji Muhammad Tahir da dai sauransu.
Baya ga haka ne Shettima ya garzaya gidan marigayi tsohon shugaban ƙasar inda ya suka gaisa da Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, kamar yadda Shugaba BolaTinubu ya umarce shi, inji shi.





