Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar Talata Mafara ta Arewa, Hon. Shamsuddeen Hassan Bosco ya bayar da tallafin karatu ga ɗalibai 100 na yankin don karanta kwasa-kwasan da suka shafi kiwon lafiya a ASB College.
Tallafin na daga cikin yunƙurin da ɗan majalisar ke yi na ƙarfafawa matasan mazaɓar sa su samu ilimin zamani.
Hon. Hassan ya kuma gabatar da tsabar kuɗi da sauran kayan tallafi ga zaɓaɓɓun mutanen da aka zaɓo daga mazaɓar sa da ya kashe sama da Naira miliyan 100 a watan da ya gabata.
Yayin da yake ƙaddamar da rabon tallafin ga waɗanda suka amfana a Talata Mafara, Hon. Hassan ya ce an yi hakan ne domin inganta yadda matasa ke ƙara ƙaimi musamman a fannin ilimin kiwon lafiya.
A cewar sa, “babban maƙasudin bayar da tallafin shine a tabbatar da cewa matasa sun tsunduma cikin harkar gina al’umma baki ɗaya”.
“Wannan matakin na da nufin samar da ci gaba da dogaro da kai a tsakanin matasa, tare da ƙarfafa gwiwar su wajen karanta ilimin kiwon lafiya don bayar da gudunmawa mai ma’ana ga al’ummarsu da ma jihar baki ɗaya”.
Da yake jawabi tun da farko, Mista Murtala Ibrahim Murcy, wanda ya jagoranci taron, ya ce wani abin nuna alheri ne, Hon. Shamsuddeen ya fara aikin da ba a taɓa yin irinsa ba a tarihin ɓangaren majalisar dokokin jihar tun 1999.”
Ya ci gaba da bayyana cewa, “ta hanyar saka hannun jari a fannin ilimi da ci gaban matasa, Hon. Shamsuddeen Hassan ya nuna matuƙar himma wajen bunƙasa rayuwar matasa wanda shi ne ginshiƙin ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
A jawabinsa na rufewa, ɗan majalisar Hon. Shamsuddeen, ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su nuna godiyar su ta hanyar zuwa makaranta sosai da kuma samun nagartaccen ilimin da ake buƙata.
Ya yi addu’ar Allah ya sa suyi fice a karatunsu kuma su kamala da sakamako mai kyau. .
Hon. Shamsuddeen ya yi alƙawarin bai wa ɗalibai 20 da suka yi fice a fannonin karatu daban-daban cikakken karramawa.
“Bayan kammala karatun ku, zamu duba fitattun ɗalibai 20 da suka samu sakamako mai kyau mu karrama su tare da ba su aikin yi”, ya jaddada cewa
