Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Malumfashi (MADA) ta jajenta wa iyalan waɗanda suka rasu a harin Masallaci da ’yan bindiga suka kai a Gidan Mantau da ke ƙaramar Hukumar Malumfashi a jihar Katsina.
Lamarin ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane guda 50.
Shugaban ƙungiyar, Malam Salisu Bawa a wata takarda, ya bayyana saƙon ta’aziyyar a ranar Asabar.
Ya ce, suna taya iyalan waɗanda suka rasu jimami da kuma fatan samun waraka cikin lokaci ga waɗanda suka jikkata.
Bawa ya kuma yi Allah-wadai da harin inda ya kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara baza jami’an tsaro a yankunan da ke fama da matsalolin ta’addanci a jihar domin ƙaurace wa faruwar irin haka a nan gaba.
Ya kuma bayyana kisan gillar a matsayin abinda aka yi bisa rashin imani da mugunta, yana mai kira ga hukumomi da su ruɓanya ƙoƙarinsu a yaƙi da ya bindiga.
Kazalika, ya yaba wa sojoji bisa hoɓɓasa da suka yi wajen ceto mutane 72 da aka yi garkuwa da su a yankin duwatsun Pauwa da ke ƙaramar Hukumar ƙanƙara a jihar.
