Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dokokin Jihar Benuwe ta ɗauki matakin dakatar da tsohon shugabanta, Aondona Dajoh.
Majalisar Dokokin Benuwe ta dakatar da Aondona Dajoh ne har na tsawon watanni uku bisa zargin ƙoƙarin tsige Gwamna Hyacinth Alia.
An dakatar da Aondona Dajoh ne yayin zaman majalisar na ranar Talaga, 26 ga watan Agustan 2025.
Dakatarwar da aka yi wa Aondona Dajoh ta biyo bayan wani ƙuduri da ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Kyan, Terna Shimawua, ya gabatar.
James Umoru daga mazaɓar Apa ya mara wa ƙudirin baya a yayn zaman majalisar na ranar Talata.
Terna Shimawua, wanda ya gabatar da ƙudurin, yana ɗaya daga cikin ’yan majalisar da Dajoh ya dakatar a ranar Juma’a da ta gabata kafin ya yi murabus daga kujerar shugaban majalisar.
Shugaban majalisar na yanzu, Alfred Berger, wanda ya yanke hukunci kan ƙudurin, ya rage dakatarwar Dajoh daga watanni shida zuwa uku ba tare da neman a kaɗa ƙuri’a kan lamarin ba kamar yadda aka saba.
Hakazalika, majalisar dokokin ta kuma tabbatar da naɗin Timothy Yangien Ornguga a matsayin kwamishina.
Timothy Yangien Ornguga, malami a fannin karatun lauya a jami’ar jihar Benuwe, na daga cikin mutanen da majalisar ƙarƙashin jagorancin Aondona Dajoh, ta ki amincewa da naɗinsu.
Sai dai, sabon shugaban majalisar, yayin da yake karanta wata wasƙa daga Gwamna Hyacinth Alia a ranar Talata, ya tantance ƙarin mutane biyar da aka naɗa.
Alfred Berger ya bayyana cewa gwamnan na da yaƙinin cewa Ornguga da James Dwem, wadanda tsohon kakakin ya ƙi amincewa da naɗinsu, ba a taba samun su da laifi a kotu ba duk da koke-koken da aka shigar kan naɗin nasu.
Abin mamaki, ’yan majalisar da a da suka yi adawa da tabbatar da nadin na su a wancan lokacin, sun yi shiru baki ɗaya lokacin da shugaban majalisar ya tabbatar da su ba tare da yin kuri’ar “eh” ko “a’a” kamar yadda aka saba ba.
Majalisar ta kuma dage dakatar da wasu masu riƙe da muƙamai guda uku da gwamnan ya dakatar a baya.
