Sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta yi ya farfaɗo da ruhin tattalin arziƙin Nijeriya – Uba Sani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamna Uba Sani ya yaba wa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan dawo da Nijeriya hayyacinta ta fuskar tattalin arziƙin da dawo wa da masu zuba hannun jari ƙarfin guiwarsu wanda ke ƙara ƙarfafa alaƙar Nijeriya da ƙasashen waje.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a hirarsa da TVC a lokacin da yake fito da irin abubuwa da Shugaba Tinubu ya cimma a ziyarar aiki da ya kai ƙasar Brazil.

Gwamnan, wanda yana cikin ‘yan rakiyar shugaban ƙasa, ya ce, ziyarar ta fito da irin kyakkyawan gobe da tattalin arzikin Nijeriya ke da ita a duniya.

“Idan ka kalli lokacin da ya hau mulki, da yawan masu zuba hannun jari na duniya ba sa don zuba hannun jari. Amma wasu daga cikin tsare-tsaren da ya kawo sun bude ƙofar damarmaki, ba kadai ga ‘yan kasuwar Nijeriya, har ma ga waɗanda suke son zuba hannun jari a faɗin duniya,” ya bayyana.

Gwamnan ya nuna cewa matakan da Tinubu ya ɗauka sun taimaka wajen cike giɓin Dala biliyan 7 domin musayar kuɗin wanda ya bai wa masu zuba jari na duniya ƙarfin gwuiwar amincewa da ƙasar nan.

Sannan gwamnan ya fito da muhimmancin ziyarar da suka kai Brazil yana mai cewa shugaban ƙasar Luiz Inácio Lula da Silva ya yi magana a kan noma da makamashi sabuntau da bunƙasa ƙwarewa da zuba jari a ɓangaren sufurin jirgin sama.

“Na yi murna ganin yadda Shugaba Tinubu ya assasa kyakkyawar alaƙa da shugaban ƙasar Brazil. Wannan dangantaka ce da aka ƙulla ta mai cike da girmamawa da buɗe ƙofar damarmaki da za a cimma a cikin kankanin lokaci.

A game da ke jihar Kaduna kuwa, gwamnan ya ce, gwamnatinsa ta mai da hankali wajen bunƙasa noma da ƙara yawan kuɗin da take kashewa noma daga kaso 0.9 zuwa 12 domin yin alaƙa da yarjejeniyar Malabo.

“Muna aiki tuƙuru domin kawo sauyi a ɓangaren noma domin samar da ayyukan yi da magance talauci da ƙara ƙwazo,” ya faɗa.

Ya kuma nuna ƙarfin guiwarsa kan ƙoƙarin da Shugaba Tinubu ke yi na bunƙasa tattalin arziki ta hanyar dabara haɗa kai da kasashen waje wanda hakan ne zai ƙara saurin cigaba da ake da fatan samu a ɓangarori daban-daban.

By ukarofi