
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dubunnan ɗaliban ƙasashen waje ciki har da ƴan Nijeriya da dama da ke karatu a Birtaniya ne aka bai wa gargaɗin ficewa daga ƙasar da zarar bizarsu ta ƙare ko kuma a kore su.
A cewar wani rahoto daga BBC a ranar Talata, ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta fara aika wa ɗalibai saƙonni ta wayoyin hannunsu na tunatar da su game da dokokin shige da fice.
Lamarin na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumomin ƙasar suka koka game da yawaitar adadin ɗaliban da wa’adin bizarsu ta ƙare kuma suke cigaba da zama a can da nufin samun mafaka.
Tuni saƙonnin suka isa ga ɗalibai kusan guda 10,000 da wa’adin bizarsu ta kusa ƙarewa.
Jami’ai sun ce, aƙalla ɗalibai 13,000 ne ake ƙoƙarin saƙonnin su ishe musu daga yanzu zuwa ƴan watanni kaɗan masu zuwa.
Wani rahoto a 2023 ya bayyana cewa kaso 15 na masu neman mafaka a ƙasar sun shigo ne ta hanyar kalar bizar ɗalibai.
