
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Matar Shugaban Ƙasa Oluremi Tinubu ta yi magiya ga ƴan Nijeriya da su bada gudumawar zagayowar ranar haihuwarta don tallafa wa aikin gina ɗakin karatu na ƙasa.
Tsohuwar sanatar, wadda za ta cika shekaru 65 a ranar 21 Satumba, 2025, ta bayyana haka ne ta wani faifan bidiyo, inda ta ce za ta sadaukar da ranar zagayowar haihuwar ne ga ubangiji a madadin yin biki na musamman domin sa.
Don haka ta roƙi al’ummar Nijeriya da su aika mata da gudumawarsu ta kuɗi a madadin katina, wainar fulawa, fulawa ko gaisuwa a jarida da sauransu.
Ta bayyana cewa, taimaka mata a kammala aikin gina ɗakin karatu na ƙasa shi ne zagayowar ranar haihuwa mafi kyau a gare ta.
Kazalika, Remi Tinubu ta ce, Ma’aikatar Ilimi ta shirya karɓar gudumawar da sunan ‘Oluremi at 65 Education Fund’ ta asusun banki kamar haka: ‘Zenith Bank Plc, 1310314977’.
