Gocewar jirgin ƙasa ya sa an yi wa hukumar NRC garambawul

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da jiragen ƙasa NRC, ta yi tankaɗe a hukumar gudanarwarta ƙasa da kwana goma da hatsarin jirgi ya rutsa da fasinjoji 20 bayan gocewarsa a a layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.

A wani saƙo da ta fitar, NRC ta ce sauye-sauyen da ta yi ya fara aiki ne tum daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025 wanda Darakta-Manajanta, Dakta Kayode Opeifa ya amince da shi.

Ta ce ta yi haka ne domin inganta ayyukan da suka shafi gudanar da tashoshin jiragen ƙasa a faɗin Nijeriya.

Al’amarin ya shafi manyan jami’an gudanarwa da daraktocin ahutoy (RDMs) waɗanda aka sauke ko kuma sauya musu wuraren aiki.

Daga cikin abubuwan da NRC ta yi akwai samar da sababbin ofisoshi guda uku waɗanda suak haɗa da na gudanar da kasuwanci da kulawa yadda ya dace (BUPED), na kula da buƙatun kwastomomi da kuma ofishin ƙididdiga.

Ana sa ran sababbin ofishinsa za su taimaka wajen inganta harkokin gudanarwa, kula da fasinjoji bisa inganci gami da bunƙasa shirye-shiryen hukumar.

By Babaji