Maulidin Nabiyyi: Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga Musulmi su gabatar da addu’o’in samun zaman lafiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A sanarwar da sakataren yaɗa labarai na gwamnan Muhammad kaula ya fitar,Gwamnan yayi wannan kalaman ne a saƙon taya musulmi murnar zagayowar tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu SAW ga al’ummar jihar.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana bikin Mauludi a matsayin wani lokaci na musamman domin gudanar da addu’o’i, da kuma ƙara jajircewa wajen bin koyarwa da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW).

Gwamnan ya jaddada cewa koyarwar Annabi Muhammad ta zaman lafiya, adalci, haƙuri, da ƙaunar juna, na da matuƙar muhimmanci wajen fuskantar ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na Maulidi wajen roƙon Allah SWT da kawo mana ƙarshen matsalolin tsaron da suka addabi Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.

By ukarofi