Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan iƙirarin cimma burin samun isassun kuɗaɗen shiga a Nijeriya a 2025, inda ya ce har yanzu ’yan Nijeriya na cikin ƙunci.
A ranar Talata, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce Gwamnatin Tarayya ta cimma burinta na samun kuɗaɗen shiga a shekarar 2025 kafin lokacin da aka tsara, inda ya kawar da batun ci gaba da karɓar bashi.
Shugaban ya ce, an samun kuɗin ne ba ta hanyar man fetur ba, inda ya ce gwamnatinsa ta samu ci gaba wajen daidaita tattalin arzikin ƙasar duk da matsin lamba ɗaga waje.
Da yake mayar da martani ga kalaman shugaban ƙasar, Obi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, ya ce idan da gaske ne batun, ya kamata a yi la’akari da rayuwar ‘yan Nijeriya.
“Shugaban ƙasar ya sanar da cewa an cimma burin samun kuɗaɗen shigar ƙasarmu na shekarar nan da watan Agusta, wanda hakan na iya haifar da daidaita tattalin arziki.”
“Ina taya Shugaban ƙasa murna. Amma mai girma shugaban ƙasa, idan har da gaske tattalin arzikin ƙasar ya daidaita kamar yadda ka bayyana, to dole ne ‘yan Nijeriya su ji a rayuwarsu ta yau da kullum, dole ne a daina karɓar rance a yanzu, a biya manyan kuɗaɗe na ‘yan kwangila, waɗanda har yanzu suke bin bashi, kuma a yanzu a samar da wasu muhimman ayyukan da ba a yi ba.
“Cibiyoyin ilimi da asibitocinmu har yanzu suna cikin mummunan yanayi, daidaiton tattalin arziki na gaskiya ba a cikin alƙalumman da aka sanar a taron manema labarai ba, amma a cikin azuzuwan da yara ke koyo, a cikin ingantattun kayan aiki da kayan aikin koyo, a asibitoci, inda ‘yan kasa za su iya samun ingantaccen kulawa, sanye take da isassun kayan aiki.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, Obi ya roƙi gwamnatin Tinubu da ta tausaya wa talakawan ƙasar, ganin yadda ta cimma burin samun kuɗaɗen shiga na shekarar.
Ya rubuta; “Bayan cimma burinmu na kuɗaɗen shiga na shekara mai zuwa, ya kamata mu nuna hankali da tausaya wa talakawan da ke cikin wahala ta hanyar tura kayan aiki zuwa wurare masu muhimmanci da za su taimaka wajen samar da ayyukan yi don rage wahalhalun da jama’a ke ciki.
