Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da inshorar lafiya a duk ma’aikatu da hukumomi (MDAs) daidai da dokar Hukumar Inshorar Lafiya ta ƙasa (NHIA) ta shekarar 2022.
Wata sanarwa da mai ba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ta ce, hukumomi za su sanya ma’aikatansu cikin shirin Hukumar Inshorar Lafiya ta ƙasa (NHIA), tare da zaɓin ɗaukar ƙarin bayanan sirri daidai da dokar.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Dukkanin hukumomi dole ne su gabatar da takardar shaidar Inshorar lafiya ta NHIA da ta bayar a matsayin wani ɓangare na takardun cancantar su,” inji sanarwar.
“Wannan takardar shaidar ta tabbatar da bin ƙa’idojin inshorar lafiya na tilas kuma tana aiki a matsayin sharaɗi na ci gaba da duk wani aiki.
“Umarnin na shugaban ƙasa ya kuma tilastawa duk hukumomi da su buƙaci ma’aikata su gabatar da ingantattun takardun Inshorar Lafiya na NHIA a matsayin wani sharaɗi na bayar da lasisi da izini.”
Hakanan an umurci NHIA don kafa dandamali na dijital don ba da damar tabbatarwa cikin sauƙi na takardun inshorar lafiya, tabbatar da gaskiya.
Mista Onanuga ya ce Tinubu, duk da haka, ya yi kira da a ƙara kusanci da kuma kyakkyawar alaƙa da kamfanoni masu zaman kansu kan wannan doka don tabbatar da cewa ba a takura wa harkokin kasuwanci ba.
