
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Ma’aikatan Fetur da Iskar Gas NUPENG, ta koka game da yiwuwar samun ƙarancin man fetur a Nijeriya, inda ta ce akwai yiwuwar mambobinta su dakatar da aiki sakamakon rikici da hukumar gudanarwar Matatar Ɗangote.
A wata takarda daga Williams Akpireha da Afolabi Olawale, wato Shugaba da Sakataren NUPENG, ƙungiyar ta zargi Matatar Ɗangote da gudanar da wasu haramtattun ayyuka akan ma’aikata wajen tauye musu ƴancin da dokar ƙungiyar ta ba su.
A cewar NUPENG, matatar ta hana direbobin da aka ɗauka aiki a ɓangaren tirelolin da ke jigilar iskar gas ta CNG shiga kowace ƙungiya ta kasuwanci, lamarin da NUPENG ta bayyana a matsayin karan-tsaye ga dokokin ƙasa.
Ta kuma yi ikirarin cewa a ranar 29 ga Agusta, 2025 takwarar kamfanin, wato MRS Oil ta fara ɗaukar direbobi aiki a wani yanayi na sharuɗɗa masu tsauri waɗanda daga ciki akwai sanya hannu akan haramta wa mutum shiga wata ƙungiya a masana’antar mai da gasa.
Akan haka ƙungiyar ta yi kira da babbar murya na a gaggauta warware matsalolin ko kuma ta tsunduma yajin aiki daga ranar 8 ga watan Satumba, 2025.
