Birtaniya ta cire ayyuka 100 daga samun bizar ma’aikata ’yan ƙasashen waje

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da tsawaita wasu sabbin takunkumi kan ɗaukar ma’aikatan ƙetare zuwa ƙasarta, tare da cire sama da guraben ayyuka 100 na ‘yan ƙasashen waje ciki har da ‘yan Nijeriya a wani ɓangare na yunƙurin da ta ke na daƙile ƙwararar baƙin haure.

Ma’aikatar Cikin Gida ta Birtaniya ta bayyana canjin manufofin a cikin wata sanarwa a shafin X ranar Asabar da safe, tana mai cewa an mai da hankali ne kan buɗe dama ga ma’aikatan Birtaniyya yayin da suke sake fasalin tsarin biza.

“Sabom tsarin zai kawo daidaiton abubuwan a ƙasar.

“Sama da ayyuka 100 ba su cancanci ɗaukar ma’aikata ’yan ƙasashen waje ba – sai dai samar da ƙarin ayyukan yi ga ma’aikatan Birtaniya. Tsarin da ya fi dacewa shi ne wadatuwar cikin gida,” inji Ofishin Cikin Gida.

Wannan manufar ita ce sabuwar matsalar shige da fice a ƙarƙashin Firayim Minista Sir Keir Starmer, wanda ya hau karagar mulki a ranar 5 ga Yuli, 2024, bayan babban zaɓen Labour wanda ya kawo ƙarshen mulkin Rishi Sunak.

Amma matakin ya jawo suka, tare da masu adawa da yin gargazin cewa zai iya zurfafa ƙarancin ma’aikata a sassa masu muhimmanci kamar kiwon lafiya da ayyukan zamantakewa.

Daga cikin ayyukan da abin ya shafa sun haɗa da ma’aikatan isar da kayan kwalliya, masu gyaran gashi, mataimakan kula da zirga-zirgar jiragen sama, jami’an soji, da masu aikin gine-gine – da dai sauran manyan ayyuka tsakanin baƙin haure.

By ukarofi