Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani sabon littafi ya yi ƙarin haske kan takun saka tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) dangane da ci gaba da tsare ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam kuma ɗan siyasa, Omoyele Sowore, duk da umarnin da kotu ta bayar na a sake shi.
Rubutun littafin na ƙunshe ne a cikin “Na rubuta abin da nake so”, wani sabon aikin da fitaccen ɗan jarida kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Richard Akinnola ya wallafa.
Littafin mai shafuka 198, wanda ya ƙunshi babi ishirin, ya ƙunshi rubuce-rubucen da Akinnola ya yi a shafin Facebook da aka fi bi da su tun daga shekarar 2017 zuwa 2025.
A cewar Akinnola, rikicin ya samo asali ne a shekarar 2019 a lokacin da gwamnatin Buhari ta ɗaure Sowore a gidan yari. Hukumar DSS ta yi watsi da sanarwar da aka bayar na sakin Sowore, inda ta jawo suka a cikin gida da waje.
A cikin littafin, Akinnola ya ba da labarin yadda suka gamu da Osinbajo inda mataimakin shugaban ƙasar na lokacin ya nuna rashin amincewarsa da matakin hukumar DSS.
Akinnola ya rubuta cewa “Na san ƙoƙarin da mataimakin shugaban ƙasa Osinbajo ya yi a baya na ganin hukumar DSS ta bi umurnin kotu, wanda kusan ya kai ga yin taho-mu-gama da hukumar tsaro, Osinbajo ya ce yana da aikin da zai koma bayan ya bar ofis, kuma ba zai iya kasancewa a lokacin da aka yi watsi da wannan umarni.”
Sai dai hukumar ta DSS, ta ce ta ja da baya kan matsin lambar Osinbajo, inda ta yi gargaɗin cewa, “ba za a iya samun shugabanni biyu ba”, lamarin da ke nuni da irin yunƙurin da Osinbajo ya ɗauka a shekarar 2018, lokacin da ya kori shugaban DSS na lokacin, Lawal Daura, a matsayinsa na muƙaddashin hugaban ƙasa.
Duk da wannan rikici, dagewar Osinbajo ya haifar da sakamako. A ranar da Akinnola ya ziyarce shi don neman a saki Sowore, an sako ɗan gwagwarmayar.
Akinnola ya bayyana cewa, baya ga maganar jama’a, sau da yawa ya kan bi tattaunawa da jama’a don ganin an sako mutanen da ake tsare da su, inda ya bayyana cewa yana da hannu a shari’ar da ake tsare da shugaban ‘yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, wanda a ƙarshe ya bayar da belinsa ta hanyar shiga tsakani.
Za a ƙaddamar da littafin ne a ranar Asabar, 13 ga Satumba, a otal din jirgin sama, Legas, a wani ɓangare na taron cika shekaru 67 na Akinnola mai taken “A Handshake Across the Niger: The Yoruba/Igbo Détente.” Aare Ona Kakanfo na ƙasar Yarbawa, Iba Gani Adams ne zai jagoranci taron.
Waɗannan bayanai sun ƙara wani sabon salo na fahimtar da jama’a kan rawar da Osinbajo ya taka a lokacin ɗaya daga cikin batutuwan da suka shafi kare haƙƙin bil’adama a gwamnatin Buhari.
