Dangote ya yi alhinin rasuwar ’yar uwar Phyna ta Big Brothers, Ruth Otabor, wacce motar kamfanin ta kashe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rukunin Kamfanin Dangote ya bayyana matuƙar alhinin rasuwar Ruth Otabor, ’yar shirin Big Brother Naija season 7, Phyna.

Ruth ta rasu ne a ranar Lahadi, 31 ga Agusta, 2025, makonni bayan wani hatsarin mota da ya rutsa da ita tare da ɗaya daga cikin manyan motocin kamfanin Dangote a kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Auchi da ke Jihar Edo.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar jim kaɗan bayan sanar da rasuwarta, kamfanin ya ce: “Mun yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar Ruth Otabor, wacce ta samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da zaya daga cikin manyan motocin mu a Auchi, jihar Edo.

Kamfanin Dangote ya bayyana cewa tun bayan afkuwar hatsarin, jami’anta da abokan aikin inshora sun tallafa wa Ruth da iyalanta, tare da biyan dukkan kuɗaɗen da ake kashewa na magani.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an shirya jigilar ta zuwa ƙasar waje domin ci gaba da kula da lafiyarta.

“Tun da hatsarin ya faru, jami’an mu da abokan aikin inshora suna tare da ita, suna biyan duk wasu kuɗaɗen magani da kuma tallafa wa danginta, an kuma shirya kai ta Indiya don ci gaba da kula da lafiyarta, tare da jiran izinin likitocin ta,” inji kamfanin.

“Abin takaici, duk da wannan ƙoƙarin da kuma jajircewar, Ruth ta rasu, mun rasa ta a yau,” inji rukunin Dangote.

Kamfanin ya sake jaddada ƙudirinsa na tabbatar da tsaro da riƙon amana a ayyukansa, yayin da ta miƙa ta’aziyya ga iyalan Otabor.

By ukarofi