Sarkin Daura ya naɗa uwargidan Gwamnan Katsina Jagaban Matan ƙasar Hausa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar ya naɗa uwargidan Gwamnan Katsina Hajiya zulaihatu Dikko Raɗɗa a matsayin Jagaban Matan ƙasar Hausa.

Naɗin sarautar ya gudana a fadan Sarkin ne bayan dawowa daga bikin sallah Gani.

Mayan baƙi da suka halarci bikin naɗin sarautar har da maigidan ta gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa tare da manyan jami’an gwamnati da yan’uwa da abokan arziki.

A jawabinsa bayan da ya jagoranci naɗin sarautar,sarkin Daura ya ce masarautar Daura ta bai wa uwargidan Gwamnan Katsina wannan sarauta saboda ƙoƙarin da ta ke yi ba dare ba rana na tallafawa matan jihar.

Ya ce wannan sarauta shine na farko da masarautar ta bada, a cewar sa masarautar tayi la’akari da irin gagarumar gudummawa da uwargidan Gwamnan ke bayarwa wajen tallafawa ba ma mata kaɗai har ba da maza a faɗin jihar.

Wannan sarautar da aka baiwa uwargidan Gwamnan ya nuna irin girmamawa da masarautar Daura ta nuna mata bisa la’akari da irin gudunmawar da take badawa wajen cigaban yankuna da tallafawa alummar jihar.

By ukarofi