DSS ta gayyaci ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore kan kalaman tunzura akan Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar ƴan sandan farin kaya DSS ta yi aiken saƙon gayyata ga ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore bisa abinda ta kira da rubutun ƙarya da ke ƙoƙarin tunzura jama’a akan Shugaba Bola Tinubu da ake zargin sa da aikatawa.

A wata takarda daga wani Uwem Davies a madadin Darakta-Janar na DSS a ranar 7 ga Satumba, an nemi Sowore da ya janye kalamansa, sannan ya bada haƙuri acikin sati guda.

Hukumar ta zarge shi da kiran mai girma Shugaba Tinubu da ‘babban mai laifi’ wato ‘criminal’ a wani rubutu da ya wallafa a kafar X ranar 26 ga Agusta, 2025.

Lamarin da ya DSS da kanta ta nemi mahukunta kamfanin sadarwa na X da ya goge shafin nasa a ƴan kwanakin da suka gabata.

Baya ga haka, ɗan gwagwarmayar ya kuma soki kalaman shugaban ƙasar na rashawa a lokacin da ya gabatar da jawabi a ƙasar Brazil.

A cewar saƙon, wajibi ne Sowore ya janye kalaman nasa akan Tinubu ta kafar da ya yaɗa su, ya wallafa saƙon bada haƙuri da neman yafiya a aƙalla manyan jaridun ƙasa guda biyu da gidan talabijin biyu, sannan ya tura wakilci ga DSS a Abuja ko ta Imel.

By Babaji