
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An tabbatar da mutuwar mutum ɗaya da samun raunuka ga wasu bakwai a yayin ruftawar wani gini a Jihar Jigawa.
Al’amarin ya auku a ranar Juma’a, a Ƙauyen Kabak da ke Ƙaramar Hukumar Kirikasamma biyo bayan mamakon ruwan sama a yankin da kewayensa.
Jami’in yaɗa labarai na majalisar ƙaramar hukumar, Musa Muhammad ya tabbatar faruwar iftila’in a wata takarda, ranar Lahadi a Dutse.
Ya ce, al’amarin ya faru ne a tsakar daren Juma’a wayewar Asabar, inda aka kwantar da mutane biyar a asibiti yayin da aka sallami sauran biyun.
Ya bayyana cewa, Shugaban ƙaramar hukumar, Muhammad Maji ya ziyarci wajen da abin ya faru tare da jajenta wa waɗanda iftila’in ya afka wa.
Haka kuma, ya bada tallafin N500,000 ga jinyar waɗanda suka jikkata da kuma N100,000 ga iyalan wanda aka rasa.
Hakan na zuwa ne wata guda bayan ruftawar wani gini a Unguwar Life Camp da ke Abuja ya rutsa da wani ɗan Nijar, wanda aka ceto shi bayan shafe sa’o’i goma a ƙarƙashin baraguzai.
