Abuja: Wike ya amince da bada takardun mallaka 374 ga masu filaye bayan gano ba su yi rajista ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Abuja Nyesom Wike ya amince da bada takardun mallaka na R-of-O da C-of-O ga masu filaye guda 374 a yankuna 15 da ke babban birnin tarayya Abuja.

Hakan ya biyo bayan gano cewa masu filayen suna amfani da su ne ba tare da karɓar takardun shaidar mallaka ba a hukumance, kamar yadda Hukumar Raya Birni FCTA ta bayyana.

A wani saƙo da FCTA ta fitar, ta ce an umarci masu filayen da kowannensu ya biya tarar Naira miliyan 5 acikin kwana 30, lamarin da zai fara aiki a ranar 10 ga Satumba, 2025.

IntelRegion ta ruwaito sunayen unguwannin da filayen suke kamar haka: “Gana Street, Maitama District; Usuma Street, Maitama District; Yakubu Gowon Crescent, Asokoro District; Aminu Kano Crescent, Wuse II District; Adetokunbo Ademola Crescent, Wuse II District; Ladoke Akintola Boulevard, Garki II District; Gimbiya Street, Garki II District; Onitsha Street, Garki II District; Ogbomosho Street, Garki I District; Lafia Close, Garki I District; Yola Street, Garki I District; Abriba Close, Garki I District; Danbatta Street, Garki I District; Ringim Close, Garki I District; and Ilorin Street, Garki I District.”

Haka kuma, hukumar ta nemi da su je reshenta na kula da lamuran filaye da ke No.4 Peace Drive a Central Area, Abuja tare da takardun filayensu na asali da katin shaida na ƙasa domin karɓar takardunsu na sabon tsarin amfani da fili.

By Babaji