Dikko Raɗɗa ya tabbatar da ƙulla yarjejeniya tsakanin gwamnatinsa da ‘yan bindiga

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sai dai gwamnan ya ce ‘yan bindigar ne suka ji wuta suka nemi ayi sulhun ba wai ita gwamnatin ce ta nemi a yi haka ba.

Ko a baya-bayan nan, an jiyo kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida yana musantawa cewa ba da gwamnatin jihar Katsina ake yin sulhu ba tsakanin al’ummomi ne da ɓarayin daji.

Tuni dai wasu ƙananan hukumomi a jihar suka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a yankunan su.

Gwamna Raɗɗa wanda ya tabbatar da haka a lokacin da yake karɓar hukuncin wata ƙungiya daga tarayyar Turai da suka kawo ziyara a jihar.

Ƙungiyar sun kawo wa jiha ɗauki na kuɗi Dalar Amurka Miliyan biyar domin tallafawa kan zaman lafiya a jihar ya ce yanzu haka akwai wasu ƙarin ƙananan hukumomi biyu da ake tattaunawa da ƴan bindigan.

By ukarofi