‘Yan sanda a Katsina sun kama wani ɓarawon mota

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a Katsina sun sami nasarar kama wani mutum Muhammad Abdullahi mazaunin Ƙofar ƙwaya, Katsina da wata mota ƙirar Toyota Corolla wanda ake zargi ya sato daga Abuja.

Motar mallakar Mr Sunday Solomon Jiyah mazaunin Abuja,yan sanda sun gano ta a wata maɓoya da ke ƙofar ƙwaya a cikin garin Katsina.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da haka yace jami’an su sun kama wanda ake zargi tare da gano motar.

DSP Sadiq Aliyu ya bayyana cewa wanda ake zargi ya faɗawa yan sandan sashin bincike,cewa shima ya karɓi motar ne daga wani da ake zargi riƙaƙƙen ɓarawon mota mai suna Abdul da aka laƙabawa suna da ‘Dukiya’ da ke zaune a ƙaramar hukumar Maluumfashi.

Kwamishinan ‘yan sanda a Katsina CP Bello Shehu ya jinjina wa jami’an sa bisa nuna ƙwarewa wajen gudanar da bincike da ta kai su ga kama Muhammad Abdullahi da ake zargi da satar motar.

Ya tabbatar wa al’ummar Jihar Katsina cewa rundunar ƴan sanda a shirye take a ko da yaushe wajen tabbatar da kare lafiya da dukiyar su.

By ukarofi