Mujaddadi Ɗanfodiyo sak ‘yan kwangila sam!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Na ga ya dace na dora alkalami don jan hankali kan wasu da su ka takarkare sai sun aibanta Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo. Aikin waɗannan mutanen na nan a kafafen sada zumunta inda su ke jefa miyagun sunaye da alaƙanta mummunan tarihi ga Shehun malamin. Waɗanda ke kwangilar nan sun tsara wata loga don samun saukin yaɗa manufofin su inda su ka rubuta “FODIYANCI SAM MUSULUNCI SAK” kuma ba ma lallai mutanen nan Musulmi ba ne don haka ba wani abun da ya haɗa su da Musulunci har ya zama sak a wajen su. Idan har musulunci sak ne wajen wadannan miyagun ba yanda za a yi su ɗauko wannan kwangilar. Wani ma in ka duba askin kan sa ka san shashasha ne da bai samu tarbiyya ba amma damar yanar gizo da ’yar wayar salula ta ba shi dama ya zagi Shehu Usmanu ya yi tsilli-tsilli da ido don ya san ya yi rasar kunya.

Tun a na abun kamar da wasa wajen ɓatanci ga mujaddadi Shehu Usmanu har abun ya zama da gaske. Masu yin wannan abun kuma su ke hura wutar ƙabilanci tsakanin Hausawa da Fulani. Haƙiƙa ba a na nufin in an ce Hausa/Fulani a na nufin Hausawa da Fulani sun narke sun zama ƙabila ɗaya ba ce, a’a manufa a nan an samu ƙabilu biyu da su ke haɗe da juna ta fuskar addini, auratayya da mu’amalar rayuwa a mazauni daya. Kazalika makiyaya da a kasari Fulani ne na kasuwanci da zolaya tsakanin su da mahauta da akasari Hausawa ne. In mu ka duba yawan makiyaya a cikin Fulani kakaf ba za su fi kashi 5% hakanan in mun duba yawan mahauta a cikin Hausawa su ma dai ‘yan tsiraru ne. Dole makiyaya na daji inda miliyoyin jama’ar da harkar su ba ce na kauyuka da birane. Wannan alakar ce ma ta sa yankin arewa ke da karfi da ya gagari hatta Turawa canja ma sa al’adu da addini. Za mu lura iyayen mu a karɓo ‘yanci daga Burtaniya su Sir Ahmadu Bello da Sir Abubakar Tafawa Balewa kan shiga London ko ma Majalisar ɗinkin Duniya daure da rawani a kan su. Zamanin su duk wannan shaƙiyancin na bambanci babu shi. A hankali yanzu wasu na nuna jihadin Shehu Mujaddadi shi ne su Bello Turji ke rayawa!. Dole ne ko in ce haƙƙi ya rataya a kan mu da sauran masu nazari mu tashi tsaye don ceto yankin mu daga masu neman kifar da shi ta hanyar murde wuyan tarihi da kawo labarun da a ka canjawa fuska a ka yi ƙarin gishiri ko ma a ka ƙirƙira don yaudarar matasa masu tasowa su ɗauka kamar wani ne a can baya ya danne mu su ‘yancin su. Idan na yi shiru kan abun da na karanta a littattafai tun lokacin da ilimi ma kyauta ne makarantu, ina ganin ban kyauta ba. Suka da furta baƙaƙen maganganu na za su sa a yi kasa a gwiwa wajen wannan gagarumin aiki ba. An so a makara kuma abun ƙalubalen wasu na shakkar yin magana don kar ‘yan bana bakwai su yi mu su dirar mikiya. Mu dai da mu ke raye yanzu a yankin arewa da ke zantawar nan a nan a ka haife mu kuma ba mu da wata kasa mu da iyaye da kakanni da ta zama gida a gare mu irin yankin na arewa. Mu taimakawa juna mu taimakawa wannan yanki ya aminta daga sharrin makirai. Ba na son kai tsaye na nuna addinin Islama a ke kai wa hari amma tabbas biri ya yi kama da mutum.  Ma’ana idan mu ka lura da kyau waɗanda ke yayata kamfen ɗin na la’antar Mujaddadi matasa ne da ba wani tarihi ko wata gudunmawa da su ka taɓa ba wa addinin Musulunci hakanan da yawa daga masu mara mu su baya ba ma Musulmi ba ne. Wasu ma daga ganin sunayen su ka san ‘yan sholisho ko ‘yan duniya hayaƙin taɓa. Duk ai’ummar da addini ba zai haɗa ta ba to akasin hakan na sharholiya zai haɗa ta. Wanda bai san tarihi ba da mai ƙarancin shekaru ka iya faɗawa tarkon waɗannan miyagun da ke iƙirarin wai kishin Huasawa su ke yi da Shehu Danfodiyo ya yaƙi kakannin su ya kwace mu su sarauta. Haƙiƙa cikin waɗanda su ka yi aikin jaddada Musulunci tare da Shehu akwai ƙabilu daban-daban. Hasalima Shehu ba manufar sa kafa runduna don yaƙar kowa ba don hatta abun da a ke cewa ya yi yaƙin ne sai bayan da a ka kai ma sa farmaki har inda ya yi hijira da almajiran sa. Asalin aikin Shehu Mujaddadi shi ne yakar yanda a ka dabaibaye addinin Musulunci da miyagun al’adu na bokanci da shirka. Hakanan jihadin ya shafi matsafa da masu bautar gumaka hatta a birnin Kano na wancan zamanin. Har dai mutum zai samu sahihin tarihin zamanin Shehu da yankunan da ya tura runduna don kakkabe miyagun aƙidu zai iya fahimtar zuwan Shehu babbar rahama daga Allah don ceto al’ummar tsohon zamanin daga zama cikin tsafe-tsafe da bautar gumaka da ma zama ƙarƙashin azzaluman sarakuna masu kashe duk wanda su ka ga dama su kwace dukiyar wanda su ka tsana. Ina fata mutane za su bi tarihin akasarin sarakunan da jihadin Shehu ya kawar za su gane me ya faru a wancan zamanin. Da yawa daga abun da ya auku a jihadin Shehu shi ne tawagar mutane da su ka rungumi kyakkyawar aƙida kan tashi su tafi wajen Shehu su nemi izini ya ba su dama don jaddada Musulunci a yankunan su. Shehu kan ba su dama da bayyana mu su ƙa’idojin wannan aiki na addini. Shi n ko kunsan akwai garuruwan da Shehu bai taɓa takawa ba a yankin arewa da sauran sassa da da’awar sat a kai? Shin ko kunsan Shehu bai samu damar zuwa Makkah don gudanar da aikin hajji ba don shagalta da ya yi da karantarwa don ceto al’umma daga halaka? Idan mu na son sanin ayyukan Shehu mu karanta littattafan sa da na ƙanin sa Abdullahi Gwandu. Bayin Allah ne da su ka share rayuwar su gaba ɗaya wajen karatu da hidima ga addini. Gaba daya ba wata sharholiya ko jin daɗin rayuwa da ke gaban su. Allah ya ƙare Shehu daga yunƙurin kashe shi da a ka yi ta yi har ya samu damar yaɗa ilimi mai tsabta da yau mu ke cin gajiya. Addinin Musulunci ba zai rayu ba tare da ilimi ko karatu da karatarwa ba bias aƙida mai kyau. Manzon Allah mai tsira da aminci ya fara da karantar da jama’a ne tauhidi don su tsaya kyam ga sanin Allah shi kaɗai ne ba a hada shi da kowa wajen bauta. Don haka duk mai wa’azi ya zama mai muhimmanci ya jaddada tauhidi don al’umma su zauna kan mikakkiyar hanya don samun rabauta a duniya da lahira. A tarihin Shehu lokacin da ya dauko wannan aiki na da’awa ya samu farmaki daga wasu sarakuna waɗanda ke ganin hakan barazana ce ga sarautar su.

Jihadin Shehu ba kasar Hausa kawai ya ratsa ba, ya shiga yankunan wasu ƙabilun daban kamar Bauchi inda Modibbo Yakubu ya kafa kasa da tutar Shehu kuma ba ma Bafulatani ba ne don haka jihadin ba yi da alaƙa da ƙabilanci kamar yanda msu murduda tarihi ke neman yayatawa. Jihadin ya shiga Gombe inda nan ma ba ƙasar Hausawa ba ce a ka samu Modibbo Bubayero ya kafa ƙasa. Jihadin ya shiga yankin da yau a ke kira Adamawa kuma ba ƙasar Hausa ba ce inda Modibbo Adama ya kafa ƙasa don aikin yada addinin Musulunci. Sassa da dama a jihadin ya shiga ba ko kamshin Musulunci gabanin isar kiran Shehu. Mu duba kiran Shehu ya shiga ƙasar Ilori wato Kwara inda ƙasar Yarbawa ce. Shigar jama’ar Shehu da auratayya tsakanin Yarbawa da Fulani ya sa har wasu masu ƙabilanci a Yarbawa ke ɗaukar su a matsayin jabun Yarbawa ko ma ba Yarbawa ba ne. Sunan su yanzu Gambari.

KAMMALAWA

Zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga mai alfarma Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya ƙarfafa ayyukan wallafa litattafan tarihi na Daular Shehu Mujaddadi. A wallafa littattafan da dama a raba su kusan kan farashi mai rahusa a faɗin Nijeriya. A rubuta litattafan da Turanci a fassara da manyan harsunan Nijeriya don mutane su gane ayyukan Shehu. Baya ga mai alfarma ina kira ga tsangayoyin tarihi kama daga jami’ar Usmanu ɗanfodio, Jami’ar Byaero ta Kano, Jami’ar Ahmadu Bello da sauran su, su riƙa shirya tarukan baje kolin tarihin abubuwan da su ka faru a arewa gabanin jihadin Shehu da bayan jihadin zuwa zuwan turawa har su ka kashe sultan na haɗaɗɗiyar Daular Attahiru a Bormi da ke yankin Funakaye a jihar Gombe. A fayyace shin a yau masu sarauta a arewa almajiran Shehu ne ko an samu sauyi? Shin in da Shehu zai dawo ya ga sarakunan da su ka zo bayan kutsowar ‘yan mulkin mallaka zai yi alfahari da su? Mun san an ragewa sarakuna ƙarfi amma har gobe ruwa na maganin ɗauda don haka su ma haƙƙi ya rataya a wuyan su, su fito da ayyukan Shehu a aikace da kakkabe masu zagon kasa kan Mujaddadi ta amfani da makircin ‘yan kwangila masu burin haddasa yaƙin basasa tsakanin manyan ƙabilun arewacin Nijeriya.

By ukarofi