Daga AISHA ASAS
Duk macen da hankali ya saukar wa za ta fara roƙon Allah miji nagari kamar yadda ta ji iyayenta na ma ta a kullum. Sai dai abin mamaki da yawa a mata idan ka tambaye su wane ne miji nagari sai ka ga amsar su ta saɓa wa sananniyar ma’anar sa.
Ban ce bai kamata ta yi addu’ar ba, hasali ma ita ce makamin da ya kamata ta riƙe tun balagar ta har sai an kaita ɗakin aure. Kafin in zayyano alamomin miji nagari, zan fara da jan kunne ga mazaje. Annabin rahma (S.A.W) ya ce “Mafifita a cikin ku su ne waɗanda suke kyautata wa iyalin su. Kuma ni ne maffifici a cikinku.” wato dai ya fi kyautatawa ga iyalinsa.
Mu kalli wannan hadisin da idon fahimta, mafifici da Annabi ya ce ya na nufin a wurin kyautata wa iyalin sa. Tambaya ta farko ita ce me ake nufi da kyautata wa iyali? Shin ana nufin ka kawo masu abinci da sutura ne kawai?
A duniyar Bahaushe kalmar kyautata wa iyali da kalmar mijin ta-ce duk ma’anar su ɗaya. A duk lokacin da aka samu namiji mai tausayi ga matarsa tare da lallaɓa ta, to ya zama mijin Hajiya. Hakan kan sa masu sauƙi a mu’amalar auratayya suke zama masu fuska biyu. Idan su na tare da matansu a keɓe sai su kyautata masu. Idan akwai idon wasu sai su zama “matayenku gonakin ku”. “Aljannar mace ta na ƙarƙashin ƙafar mijinta, idan ba ta bauta ma shi ba ta dawamma a wuta.”
Da yawa a cikin masu ilimin zamantakewar aure jahilai ne. idan ba don da jahilci ba da ka dafa wa matarka abinci ko da a gaban idon mahaifiyarka ce. Da ka riƙa ma ta jaka kun bi hanya. Da ka rarrashe ta ko a gaban waye. Da ka ɗauki ɗanku don rage mata ɗawainiya.
Mai ilimi ne kawai ya san ba kasawa ba ce ko zama mijin Hajiya. Ya amince da yin hakan ne jarumta da ƙima tare da nuna cika namiji, dalili ya karanta ya ji yadda fiyayye a halitai, mafi daraja a wurin Allah Annabi Muhammad (S.A.W) yake rayuwa da matansa.
Shin za ka iya haɗa kanka da shi wurin matsayi da jarumta? Nesa ya fi ka, amma ya yi wasa da matanshi, ya rarrashe su, ya kuma taya su aikace-aikacen gida.
Maigida misali zan ba ka ƙissar da ta zo da bayanin wani lokaci da manzon rahma ya yi dare bai dawo gida da wuri ba. A lokacin kwanan Nana Aisha (R.A) ne. Lokacin da ya iso sai ya tarar ta rufe ƙofa. Ya buga don ta buɗe, amma sai ta ce ba za ta buɗe ba don ya yi dare, ma’ana dai ta yi fushi. Kun san me Annabin Allah ya yi? Cikin tattausar murya ya dinga rarrashin ta ta ƙofar tare da kalamai masu sanyaya rai har sai da ta huce ta buɗe ƙofar.
Idan kaine fa? Ina ganin ashar da za ka dinga ɗura ma ta har maƙota sai sun ji. Idan ta yi sa’a ka haɗa da saki. Ko ka haura ta katanga ka ma ta ɗankaren duka, sannan ka korata gidan tsohonta, kai nan ka yi maganin marar kunya.
Wane ne Miji nagari?
1. Shi ne mai yi wa matarsa uzuri a kan raunin ta: Ka dawo gida bayan ka biya shagon abokin ka mai sayar da turare, hakan ya sa ka shigo ka na ƙamshi mai tashi da daɗi. Sai matar ka ta ɓata rai, cikin fushi ta tuhume ka da biya wa wurin wata har ta feshe ka da turare. Kuma duk yadda ka so ka fahimtar da ita ta ƙi sauraron ka, ta ƙi ba ka abinci, idan ka ce ruwan sha, ta ce ka je wurin wadda ta sanya ma ka turare ta ba ka. Ka da ka ɓata fuska, yi murmushi gare ta, sannan ka yi ma ta uzuri. Ka sa wa ranka raunin ta ne.
2. Shi ne wanda ya ke zame wa matar shi kwanciyar hankali: Yake zame ma ta gida da ba za ta damu da muhallin duk da za ta zauna ba matuƙar ta na tare da shi.
3. Shi ne wanda bai zame wa matar sa wani yaƙi da za ta tunkara ba, wanda ake fatan duk runtsi ta yi nasara.
4. Shi ne wanda ba ya kushe buƙatar matarsa, ya kan rarrashe ta yayin da ya ji buƙatar ta. Ya kan nuna muhimancin abin da ta ke so wurin sa. Bari in ba mu misali da abin koyin mu Annabin Allah (S.A.W), a cikin wata ƙissa an bayyana wata tafiya da ya yi da Safiya (R.A) sai ta fara kuka, a cewar ta wai an ɗaura ta a raƙumin da ba ya gudu. Sai ya share ma ta hawaye, ya rarrashe ta, sannan aka kawo ma ta wani raƙumin.
5. Shi ne wanda yake wasa da matarsa don nishaɗi. Hadisi ya tabbatar Manzon Allah (S.A.W) ya na yin wasan tsere da matarsa Nana Aisha (R.A). Shin ka taɓa wasa da matarka da ta wuce ta fatar baki?
6. Shi ne wanda ke yawan yi ma ta godiya a cikin hidindimu da ta ke yi ma sa: Ka dawo gida ka taras da ko’ina a tsaftace. Ga abincinka na jiran isowar ka. Yana da kyau ka kalle ta da murmushi ka yi ma ta godiya. Sannan ka ƙara a lokacin da ta zuba ma ka abinci. Ka ƙara wata yayin da cikinka ya tabbatar da ƙoshin sa. Abin haushi malam Bahaushe bai san godiya ga matarsa ba. Abin da kawai take samu a matsayin na ci, ko na gani shi ne, ƙorafin gishiri ya yi yawa, ko kin cika yaji kamar ki na son kashe ni, ko a daina samun albasa a salad. Abin da maigida ya kasa fahimta shi ne, yawan godiyarka ga matarka, da yaba ma ta, yawan ƙarin kyautatawar da za ta yi ma. Godiya ga mace tamkar ƙara mai ne a mota, ta yi ta gudu da kai har ta kai ka muhallin da ka ke da muradin zuwa. Kyautatawar da ta ke yi ma ka za ta ƙaru a lokacin da ka ke gode ma ta da yabawa. Amma idan ka zama malam ƙorafi, to sai ka wayi gari ka nemi duk kyautatawar ka rasa, ko za ka yi hauka don masifa ba za ta dawo da ita irin ta farko ba, domin dai a na ta furucin ko ka yi ba tsira za ka yi ba. To ai gara ma ta san ba ta yi ba.
Za mu cigaba a mako mai zuwa.
