Forest ta naɗa Postecoglou a matsayin sabon kocinta

Spread the love

Nottingham Forest ta sanar da naɗa Ange Postecoglou a matakin sabon kocinta, bayan da ta kori Nuno Espirito Santo.

Nuno ya bar City Ground a tsakar daren Litinin, bayan wata 21 yana jan ragama da yin wasa uku da fara kakar bana ta Premier League.

Postecoglou ya koma aikin horar da tamaula a Premier League, bayan wata uku da Tottenham ta kore shi, sakamakon da ta kare a mataki na 17 a kasan teburin Premier League.

Sai dai mai shekara 60 ya lashe Europa League a ƙarshen kakar da ta wuce, hakan ya kawo ƙarshen tsawon shekaru ba tare da babban kofi ba.

Yanzu dai Forest tana mataki na 10 a teburin Premier League, bayan wasa uku da fara kakar nan.

Wasan ƙarshe da Nuno ya ja ragama shi ne wanda West Ham ta je ta doke Forest 3-0 a cikin watan Satumba a Premier League.

Mai shekara 51 ya karɓi aikin horar da Forest a cikin Disambar 2023, wanda ya maye gurbin Steve Cooper.

A kakar da ta wuce ya kai Forest mataki na bakwai a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila – mataki mai ƙyau tun bayan 1994/95 da samun tikitin shiga gasar zakarun Turai – karon farko cikin shekara 30.

By ukarofi