Sabunta tsarin koyarwa a zamanin AI

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A makon da ya gabata aka gudanar da bikin ranar yabawa da muhimmancin karatu da rubutu a rayuwar ɗan adam wanda aka gudanar a ƙasashen duniya da daban-daban.

Hukumar Majalisar ɗinkin Duniya ta UNESCO ce ta tsayar da wannan rana ta takwas ga watan Satumba, bayan babban taron manyan ministocin ilimi na duniya da aka yi a ƙasar Iran, a shekarar 1966, da nufin ƙarfafa gwiwar ƙasashe su himmatu kan harkar ilimi da yaƙi da jahilci a tsakanin manya da yara.

A bana bikin ranar ya mayar da hankali ne kan yadda za a yi aiki da fasahar sadarwa ta zamani ta hanyar amfani da harsunan gado don samar da ilimi, musamman a ƙauyuka da yankunan da
ba sa samun kulawar hukumomi.

ƙudiri na huɗu na Majalisar ɗinkin Duniya na SDG ya mayar da hankali ne wajen ƙoƙarin samar da ilimi ga kowa da kowa, maza da mata, manya da yara, na birni da na karkara, kafin nan da shekarar 2030. Kodayake har yanzu samar da ilimi a birane ma na fuskantar ƙalubale ballantana kuma a ƙauyuka, inda babu wadatattun ajujuwan karantarwa, babu ƙwararrun malamai, babu wayewa kan neman ilimin kansa. Lura da yadda akasarin iyaye ba su samu damar yin karatun ba, ballantana kuma su ƙarfafa gwiwar ’ya’yan su ko tallafa musu don su tsaya su yi karatun.

A wannan zamani na ci gaban fasahar sadarwa inda ake amfani da manhajoji na karantarwa da neman Ilimi, da bayyanar fasahar zamani ta Artificial Intelligence (AI) za a iya cewa an shiga cikin wani sabon mataki a harkar koyarwa da neman Ilimi. Shiga ɗakin karatu, ko ɗaukar littafi don yin karatu ya fara zama tsohon yayi, musamman a tsakanin matasa. Kodayake ba kowanne ɗalibi ba ne ke da zarafin samun damar amfani da babbar waya don bincike kan wani sabon bayani na ilimi ko aikin makaranta.

An fara ƙarfafa amfani da tsarin neman ilimi daga gida wanda a turance ake kira da distance learning ne, tun lokacin da duniya ta fuskanci ɓarkewar annobar Kwarona, a tsakanin shekarar 2020. Lokacin da aka rufe makarantu da kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a, domin rage tasirin cutar da daƙile yaɗuwar ta. Sakamakon yadda zaman kulle ya haifar da koma-baya a harkar ci gaban ilimi, ya sa makarantu da dama suka ɓullo da tsarin karantarwa daga gida, ta hanyar amfani da wayoyin hannu ko ta hanyar internet.

Wannan tsari ya taimaka wajen samar da ƙarin wasu dabaru da hanyoyin koyarwa ko yaɗa ilimi ta manhajoji da ake saukewa ta wayoyin hannu da ta kwamfiyuta. Daga ciki akwai wata manhaja da wani kamfanin sadarwa da ke Jos a Jihar Filato, da haɗin gwiwar wasu turawa daga Jami’ar Georgia ta ƙasar Amurka suka ƙirƙiro, mai suna EDUBOT, wacce take aiki da fasahar AI. Wannan manhaja a cewar waɗanda suka ƙirƙiro ta bata buƙatar data wajen sarrafata. Sannan babban aikin ta shi ne fassara ayyukan ilimi da zuwa wasu harsuna na gida, domin sauƙaƙawa ɗalibi fahimtar abin da ake koya masa.

Na samu halartar taron ƙaddamar da wannan sabuwar manhaja, inda kuma na saurari bayanan yadda tsarin gudanar da fasahar yake, da yadda ake ƙoƙarin shigar da manyan harsunan Nijeriya uku, da suka haɗa da Hausa, Yoruba, da Ibo. Yayin da kuma ake sa ran tattara muhimman bayanai da suka shafi wasu ƙananan harsuna na ƙabilun Filato su ma a cik, da nufin bai wa kowanne mutum damar koyon ilimi a duk inda yake. Wannan tunani shi ne ya zo daidai da manufofin Majalisar ɗinkin Duniya na samar da ilimi ga kowa ta amfani da harsunan gado na uwa, don a samu nasarar yaƙi da jahilci a ko ina a duniya.

Fitowar fasahar zamani ta AI ya ƙara sauƙaƙa yadda duniya za ta iya cimma wannan buri kafin nan da 2030, amma har idan gwamnatoci sun yi hoɓɓasa wajen ganin an samar da tsarin koyar ilimin fasahar sadarwa ta ICT, tun daga matakin farko na ilimi, sannan su ma malaman da suke koyarwa a ƙara musu horo da ilimi na yadda za su samu dabarun koyarwa cikin sabon tsarin da duniya ke yayi, yadda za su tafi tare da zamani. A inganta makarantun ƙauyuka da samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ta yadda za a iya amfani da na’urorin da za a yi aiki da su wajen koyarwa.

Lallai ne kuma hukumomi su ƙara ƙarfafa gwiwar al’ummomin su ta hanyar samar da ilimi kyauta da bunƙasa tallafin karatu da ake bayarwa, ta yadda za a ɗauke wa iyaye nauyi da fargabar yadda za su samar wa ’ya’yansu ilimi, a yayin da ake ciki na tsadar rayuwa da karyewar tattalin arziƙi.

Yana da kyau sosai a ƙarfafa gwiwar marubuta wajen amfani da harsunan gado cikin rubuce-rubucen su, da samar da littattafai na yara da na yaƙi da jahilci, irin waɗanda marubuta irin su marigayi Dr. Abubakar Imam da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya suka samar, waɗanda aka riƙa amfani da su a ƙoƙarin da aka yi na yaƙi da jahilci a Arewa.

Lallai kada mu bari a bar jihohin mu da yankin mu na Arewa a baya wajen amfani da wannan dama ta fasahar zamani a harkokin mu na ilimi, domin al’ummar mu ta ƙara samun wayewa kuma a tafi da ita a kowane tsari na ilimi da ƙirƙira.

By ukarofi