
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙwararre akan harkar shari’a, Emmanuel Umahi Ekwe (Esq), ya caccaki Majalisar Dattawa bisa hukuncinta na ƙara wa’adin dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan akan wata shida da aka yi mata tun a watan Maris.
A wata sanarwa da ya fitar wa Blueprint a yau Lahadi, Umahi ya bayyana hakan a matsayin abinda aka yi ba bisa doka ba, lamarin da ya kira da saɓa wa dokokin ƙasa da na mulki.
A cewarsa, sashi na 66(5) na kundin doka na 1999, ya taƙaice wa’adin dakatarwar da za yi wa jami’an gwamnati, yana mai cewa tuni Natasha ta kammala na wata shida da aka yi mata a hukumance, wanda ya ba ta ƴancin komawa bakin aiki.
Ya ce, cigaba da tafiya a matsayin dakatacciyar sanata a gare ta ba tare da bin hukuncin kotu ba tauye ƴancinta ne da dokar ƙasa ta ba ta.
Don haka ya kirayi jagorancin majalisar da ta girmama matsayin shari’a tare da gaggauta ƙyle sanatar ta dawo bakin aiki.
Ya kuma yi gargaɗin cewa matuƙar majalisar ta cigaba bijire wa kiran, hakan ka iya zama barazana ga dimukraɗiyyar Nijeriya da babban ƙalubale ga zaɓaɓɓun ƴan siyasa.
