Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Rundunar sojojin Najeriya ta 1 Brigade Gusau, ta rabawa manoma 100 taki kyauta a Jihar Zamfara, a wani ɓangare na dabarun yaƙi da ta’addanci, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Kwamandan Brigade ɗin, Brig. Janar Mustapha Jimoh wanda mataimakin shugaban ma’aikatan Rundunar Sojin, Laftanal Kanal Isah Galadima ya wakilta a lokacin rabon ya bayyana cewar, an gudanar da wannan shiri ne domin bunƙasa samar da abinci da kuma ƙarfafa dangantakar jama’a da rundunar sojoji.
“Ba ko yaushe muke ɗaukar makamai ba domin yaƙi da ta’addanci, muna amfani da hanyoyin da dabarun kawo ƙarshen matsalar tsaro ba tare da ɗaukar makamai ba don ƙarfafa samar da aminci a tsakanin al’umma musamman ta samar da abinci, kayan ilimi, aikin jinya, da tallafawa al’ummomi don samun kyakkyawar fahimta,” in ji Galadima.
Ya jaddada cewa shirin ya yi daidai da manufar jagoranci na babban hafsan soji na ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, wanda ke ba da fifiko ga samar da zaman lafiya tare da ayyukan tsaro.
Haka zalika wakilin mu ya tattaro cewar, an zaɓo waɗanda suka amfana daga ƙauyukan ƙaramar hukumar Tsafe da suka haɗa da Gidan-Giye, Kucheri, Magazu, Bilbis, da Fegin-baza.
Rundunar sojin ta yi gargaɗi ga manoman dasu guji karkatar da takin, inda ta buƙaci manoma da su yi amfani da shi cikin adalci domin cimma nasarar da ake so.
Mai martaba Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammad Bawa, wanda babban hakimin yankin, Alhaji Abubakar Aliyu (Sarkin Garbas) ya wakilta, ya bayyana jin daɗinsa, inda ya bayyana tallafin ga manoma a matsayin lokacin da ya dace saboda ƙarancin taki a bana.
Shima da yake jawabi mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Tsafe Hon. Sani Abdullahi, ya bayar da tabbacin cewa majalisar ƙaramar hukumar za ta sanya ido kan yadda ake amfani da shi domin tabbatar da cewa manoman da suka amfana sun yi amfani da takin yadda ya kamata.
Da yake jawabi a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, Malam Abubakar Magaji Marafa, ya godewa rundunar sojin bisa wannan karimcin da aka yi musu, inda ya yi alƙawarin yin amfani da takin yadda ya kamata.
