Filato: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan majalisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga Jihar Filato sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar mazaɓar Pankshin ta Kudu, Hon. Denty Laven.

A cewar rahotannin, an yi garkuwa da shi ne a gidansa da ke yankin Dong a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Jihar Filato na fuskantar ƙalubale a fannin al’amuran tsaro a ƴan kwanakin nan, inda haka ya sa jami’an tsaro suke ta ƙoƙarin shawo kan al’amarin.

A makon da ya gabata ƴan bindiga suka shiga unguwar, inda suka yi garkuwa da ɗan hidimar ƙasa na NYSC da wani ɗalibin Jami’ar Jos.

Al’amarin ya auku ne a lokacin da ƴan bindigar suka kutsa gidan Solomon Dansura da misalin ƙarfe 10 na dare tare da tserewa da matasan baƙin nasa guda biyu.

Saida ba a samu wani bayani daga jami’an gwamnati ko ofishin ƴan sanda ba a yayin kammala rahoton.

By Babaji