
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar ƴan sandan farin kaya DSS, ta gayyaci tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Ibrahim Malami akan mummunan harin da aka kai wa tawagar motocinnsa a Birnin Kebbi, farkon watan nan.
Rahotanni sun bayyana cewa, Malami, wanda shi ke jagorantar tafiyar jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi, an masa tambayoyi ne a ofishin DSS na jihar da ke Birnin Kebbi.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da Malami da tawagarsa ke komawa daga gida bayan sun je ta’aziyyar rasuwar Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dakta Bello Halliru.
A yayin haka ne aka lalata motoci da adadinsu ya kai kimanin goma da raunata wasu magoya bayansa, lamarin da ya haddasa cecekuce musamman a fagen siyasa.
Da yake jawabi a wank saƙo, Malami ya ce gayyatar ta DSS an yi ta bisa mutuntawa, inda ya yaba wa jami’an kan yadda suka nuna ƙwarewa wajen tattaunawa da shi.
Da fari Malami, ya yi zargin cewa harin na da alaƙa da siyasa daga ɓangaren ƴan adawarsa da nufin haifar masa da magoya bayansa tsaiko a harkokinsu.
Lamarin da ya sa jam’iyyar APC a jihar ta nesanta hannunt a ciki, duk da cewa Malami ya yi wa rundunar ƴan sanda da DSS ƙorafi akan faruwar al’amarin.
