Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa ta buɗe ofishin Natasha bayan wata shida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa ta buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke sashe na 2.05 a majalisar.

Mataimakin Daraktan majalisar, Alabi Adedeji ya yi haka a yau Talata, lamarin da ya ba Sanatar, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya damar komawa bakin aiki a ranar 7 ga watan October, 2025.

A watan Maris, 2025 aka dakatar da ita bayan rikici da zauren majalisar akan batun wajen zama da aka ware mata a ranar 20 ga watan Fabarairu, 2025.

Majalisar ta zarge ta da taka dokar tsayuwa sannan ta dakatar da ita na tsawon watanni shida, lamarin da ya haramta mata shiga dukkan harkokin majalisar.

Duk da cewa ta ƙalubalanci hakan a kotu, majalisar ta yi buris da kuma cigaba tsayawa akan matsayarta.

Sannan, Natasha ta musanta zargin da aka yi akan nata da ya sa aka dakatar da ita, inda ta yi ikirarin cewa matsala ce ta jinsi ko kai-da-kai, saidai jami’an majalisar sun tirje akan taka wasu dokokin majalisar ya sa aka ɗauki matakin akanta.

By Babaji