NSCDC ta sami sabon kwamanda a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Abbas Ɗan Ale Moriki shine sabon kwamandan hukumar tsaro na farin kaya (Civil Defence) a Jihar Katsina.

Wata sanarwar da jami’in hulɗa huɗɗa da jama’a na hukumar a Katsina SC Buhari Hamisu ya fitar, sabon kwamandan ya canji Kwamanda Aminu Datti Ahmad da aka yiwa sauyin wajen aiki.

A jawabinsa na ban kwana kwamanda Aminu Datti ya yabawa jami’an hukumar a Katsina bisa irin goyon baya da suka bashi ya gudanar da aikin sa a jihar.

Sai yayi kira ga jami’an hukumar da su ba sabon kwamandan irin goyon bayan da suka bashi domin samun nasarar tafiyar da aiki a jihar.

Da yake jawabi bayan da ya amshi ragamar shugabanci kwamanda Abbas Moriki ya yaba da irin salon shugabanci irin na babban kwamnada na ƙasa Farfesa Ahmad Abubakar Audi ke nunawa na tabbatar da kare muhimman wuraren gwamnatin tarayya.

Ya tabbatar wa gwamna Dikko Raɗɗa da cigaba da taimakawa wajen samar da tsaro a muhimmin wurare na gwamnatin tarayya da Jihar Katsina baki ɗaya.

Sabon kwamandan ya rike muƙamai daban daban a hukumar a jihohin Kano, Sokoto, Zamfara,Jigawa da Kaduna kafin isowar sa Katsina.

Yayi karatun digiri na ɗaya da na biyu a jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto.

By ukarofi