Gwamnatin Kano ta ɗauki ƙarin malamai fiye da 4,000

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

A ƙoƙarinta na inganta da farfaɗo da harkar ilimi tun daga tushe, gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ta ɗauki ƙarin malaman makarantar firamare guda 4,315, domin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin malamai a makarantu a faɗin jihar.

Da yake mika takardun aikin na dundundun ga sabbin malaman a ɗakin taro da ke filin wasa na Sani Abacha, ƙofar Mata, Kano, Gwamna Abba ya ja hankalin sabbin malaman da su rungumi aikin da gaskiya da riƙon amana tare da zama jakadun hali nagari ga ɗaliban da za su koyar.

Gwamnan ya bayyana cewa tun zuwansu mulki, gwamnati ta ɗauki malamai 5,000 a shekarar 2023, sannan a 2024 ta sake ɗaukar 5,632. A bana kuma an sake ɗaukar ƙarin 4,000, duk ƙarƙashin shirin BESDA, domin inganta harkar ilimi a jihar.

Domin ƙarfafa ƙwazon malamai, Gwamna Abba ya sanar da shirin ɗaukar ƙarin malaman 2,616 tare da kaddamar da tsarin bayar da rance mara ruwa ga malamai, mai darajar naira biliyan biyu. Ya kuma amince da raba babura 414 da kwamfutoci 300 ga malaman domin inganta koyarwa.

Haka zalika, Gwamnan ya bayar da umarnin sake buɗe makarantar firamare ta kwana a garin Minjibir mai ɗaukar ɗalibai 180, tare da ɗaukaka matsayin makarantar ƙaramar hukumar Ungogo zuwa kwana, wacce za a samar mata da kayan aiki na zamani. Ya kuma bayyana shirin ɗaukar 17,000 na masu gadi domin kula da kayan makarantu a faɗin jihar.

Injiniya Abba ya ƙara da cewa jajircewar da gwamnatinsa ke yi wajen gyara da inganta ilimi na ƙara nuna tasiri, inda jihar ta zama kan gaba a sakamakon jarabawar NECO na bana. Ya ce hakan hujja ce cewa gwamnatinsa ta ɗauki harkar ilimi a matsayin ginshiƙin cigaban al’umma.

By ukarofi