Ban ƙullaci kowa a raina ba – Jonathan ya yi wa’azin yafiya a taron rasuwar Audu Ogbeh

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ba ya jin haushin kowa kan taƙaddamar siyasa a baya ko kuma kai hari, yana mai jaddada cewa afuwa, tawali’u, da sasantawa na da matuƙar muhimmanci ga haɗin kan Nijeriya da ci gaban dimokraɗiyya.

Jonathan ya bayyana hakan ne a yammacin Larabar da ta gabata a Abuja yayin wani taro na karrama marigayi Audu Ogbeh, tsohon ministan noma da raya karkara kuma wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ikechukwu Eze ya aike wa Manhaja, tsohon shugaban ƙasar ya bayyana Ogbeh a matsayin mutum mai son zaman lafiya da tawali’u da yafiya, wanda ya kamata kimarsa ta zama abin koyi ga shugabannin Nijeriya.

Jonathan ya ce “Cif Ogbeh mutum ne da bai nemi fansa ba, ya yi imanin cewa ya kamata a bar abin da ya gabata a baya kuma dole ne mu ci gaba.”

“Ta haka, ya kasance kamar ni, idan kun cutar da ni a yau, zan gafarta muku. Ba na jin haushin kowa. Na yi imani cewa abin da ya wuce ya wuce, kuma na ci gaba.”

Jonathan ya ba da labarin yadda dangantakarsa da Ogbeh ta kasance tun farkon rayuwarsa ta siyasa a jihar Bayelsa.

“Ban san Cif Ogbeh ba sai da na zama mataimakin gwamna a lokacin da yake riƙe da muƙamin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, a wancan lokacin, mataimakan gwamnonin ana yawan kallona a matsayin tayoyi, amma ya ɗauke ni a matsayin amini,” inji Jonathan.

Ya tuna da ziyarar da ya kai Ogbeh a Abuja, ya kuma yi doguwar tattaunawa mai ma’ana, ko da ya hau kujerar shugaban ƙasa.

Jonathan ya ƙara da cewa “Duk lokacin da yake son ganina yakan zo, wani lokacin kuma mu kan shafe sa’a guda muna tattaunawa kan al’amuran ƙasa.”

Tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci ‘yan siyasar Nijeriya da su yi koyi da ɗabi’un Ogbeh, yana mai cewa tawali’u, yafiya, da gina gada na da matuƙar muhimmanci wajen magance rarrabuwar kawuna a siyasance da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Kiran na Jonathan ya yi daidai da nasa falsafar siyasa, musamman wanda aka nuna a shekarar 2015 lokacin da ya amince da shan kaye a hannun Muhammadu Buhari cikin lumana a zaɓen shugaban ƙasa, matakin da ake ganin ya hana tashe-tashen hankula a ƙasa da kuma kare dimokuradiyyar Nijeriya.

Cif Audu Ogbeh, wanda ya rasu a ranar 9 ga Agusta, 2025, a Abuja, ya kasance jigo a siyasar Nijeriya. A matsayinsa na shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa tsakanin 2001 zuwa 2005, ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara siyasar jam’iyya a jamhuriya ta huɗu.

Daga baya ya riƙe muƙamin ministan noma a ƙarƙashin Shugaba Buhari, inda ya zaburar da sauye-sauyen harkokin noma, da samar da abinci, da kuma inganta harkokin noma wadanda suka bar tarihi mai dorewa ga tattalin arzikin Nijeriya.

Jonathan ya yaba da gudunmawar Ogbeh, inda ya kwatanta shi a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda ya yi rayuwar hidima, tattaunawa, da kuma haƙuri.

By ukarofi