Daga UMAR GARBA a Katsina
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruƙ Umar, ya ba wa fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu Rarara sarautar Sarkin Waƙar ƙasar Hausa, lamarin da wasu za su iya kallo a matsayin wani huce-haushi biyo bayan badaƙalar ba wa mawaƙin digirin girmamawa na ƙarya.
Naɗin na zuwa ne a yayin da jama’a ke yin ta cece-kuce game da karramawar da wata jami’a mai suna European-American Uniɓersity ta janye wa fitaccen mawaƙin bayan an ba shi digirin girmamawa na dakta.
Reshen jami’ar da bayanai a yanar gizo suka nuna cewar, hedikwatarta ta ƙasar Faransa ce ta yi bikin karrama mawaƙin a Abuja a ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025, taron da ya samu halartar wasu fitattun mutane.
Sai dai =’yan sa’o’i bayan kammala bikin da aka yi, jami’ar da ake alaƙanta wa da Turai da Amurka ta fito ta ce, ba ta san zancen ba, domin ba da yawunta aka miƙa wa fitaccen mawaƙin siyasar digirin na girmamawa ba, kazalika dukkanin mutanen da suka yi iƙirarin alaƙanta kansu da jami’ar ta barranta da su, domin sun yaudari mutane ne da sunanta, don samun damar karɓar na goro kamar yadda jami’ar ta bayyana a shafinta na yanar gizo.
Sai dai a martanin da Rarara ya mayar game da wannnan batu ya ce, bai ba wa wani ko wata kuɗi ba, don a ba shi wannnan digirin girmamawa ba da ake ta cece-kuce a kai ba. Fitaccen mawaƙin ya ƙara da cewa, duk da jami’ar ta nisanta kanta daga batun ba shi digirin (Dr) zai so mutane su cigaba da kiran sa da “dakta”, saboda ya sauke Alƙur’ani mai girma.
A nan gaba kaɗan ake sa ran gudanar da shagalin bikin tabbatar da naɗin Dauda Kahutu Rarara a masarautar Daura a matsayin Sarkin Waƙar ƙasar Hausa.
