Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
An kama wata mata da ake zargin tana zana jarrabawar makarantar ‘Chartered Accountants of Nigeria’ (ICAN) a madadin Sarah Enoch Adi, Kwamishiniyar Kuɗi ta Jihar Taraba.
A wani faifan bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa, masu kula da jarrabawar sun yi wa wadda ake zargin tambayoyi, inda ta bayyana kanta da Leaɓitt Feliɗ. Sai dai bayanai sun nuna cewa ɗalibar da ta yi rijistar wannan jarrabawar ita ce kwamishina Sarah Enoch Adi.
Lokacin da masu kulawa suka matsa mata, Feliɗ ta faɗi cewa tana rubuta jarrabawar ne a madadin Sarah Adi. Da aka nemi sunan ta, ta ce, “Leaɓitt Feliɗ.”
Masu sa ido sun lura da rashin daidaituwa tsakanin maganganunta da cikakkun bayanai.
Ko da yake Feliɗ ta yarda cewa ta zana jarrabawar don wata ne, ta musanta sanin Sarah da kanta. Ta yi iƙirarin cewa wani mai suna Joshua ne ya ɗauke ta aiki, amma ta ce ba ta san sunan sunansa ko kuma inda yake aiki ba.
Jami’an jarrabawar sun yi gargaɗin cewa za a iya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda idan ta kasa yin ƙarin bayani.
“Duk bayanan da muke samu a nan… za mu sami wasu bayanai biyu daga ‘yan sanda,” inji wani mai sa ido. “Muna so mu sauƙaƙa. Don haka, idan kin ba mu bayanin, za ki iya tafiya kawai, babu buƙatar ɓata lokaci.”
Wannan dai na ɗaya daga cikin rigingimun da ke tattare da kwamishinar tun bayan naɗa ta. A watan Agusta, ma’aikatan gwamnatin jihar Taraba sun buƙaci gwamna Agbu Kefas da ya kori Akanta Janar na jihar, Gauis Danjuma, da kwamishiniyar kuɗi, Misis Adi, bisa zargin tafka kura-kurai a aikin tantance ayyukan kuɗin mutane.
