Muna yaba wa Gwani Makoɗa kan sakamakon NECO da ɗaliban Kano suka yi zarra – Hon. Doguwa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Jagoran siyasar ƙaramar Hukumar Doguwa kuma mai ba wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf shawara kan dabarun tafiyar da siyasa, Hon. Ali Abdu Dogowa, ya bayyana cewa, nasarar da Kano ta samu a sakamakon jarrabawar kammala sakandire na hukumar shirya jarrabawa ta NECO babbar nasara ce ga al’ummar Kano da Arewa bakiɗaya.

Hon. Dogowa ya jaddada cewa wannan nasara ta samo asali ne daga jajircewar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, tare da kulawar Ma’aikatar Ilimi ƙarƙashin jagorancin Hon. Gwani Ali Haruna Makoɗa, wanda ya taka rawar gani wajen gyara tsarin ilimi a jihar.

Haka kuma, ya jinjina wa gwamnatin Kano bisa raba takardun aiki ga malamai fiye da dubu huɗu ƙarƙashin shirin BESDA a makon da ya gabata, wanda ya bayyana a matsayin gagarumar nasara ga ma’aikatar da gwamnati. Ya bukaci waɗanda aka ɗauka aikin da su riƙe amana tare da gudanar da ayyukansu da ƙwazo da jajircewa.

A ƙarshe, Hon. Dogowa ya yaba wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, bisa jajircewarsa wajen kawo cigaba a fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar Kano.

By ukarofi