
Matatar fetur ta Ɗangote ta sanar da dakatar da sayar da fetur da ‘Naira’, lamarin ƴan kasuwa ke ganin ka iya shafar farashinsa da matsi ga kuɗaɗen cinikayyar ƙasashen waje.
Kamfanin ya ce daga ranar Lahadi 28 ga watan nan na Satumba, zai koma sayar da tataccen mansa a kan farashin Dala.
Wata sanarwa da ya fitar wa kwastomominsa, kamfanin ya bayyana cewa yin hakan ya zama wajibi saboda yarjejeniyar da suka ƙulla na sayar masa da ɗanyen man Nijeriya akan farashin Naira ya zo ƙarshe.
A saboda haka ne ya ce zai dakatar da sayar da tataccen man nasa a farashin Naira.
