
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an tsaro na haɗaka (CJTF) reshen Arewa ta Gabas da ke aiki ƙarƙashin atisayen Haɗin Kai, sun yi nasarar daƙile ayyukan jigilar wasu kayan aiki ga mayaƙan Boko Haram da na ISWAP tare da kama wasu da ake zargi akan haka a jihohin Borno da Adamawa.
A tsakanin ranakun 19 da 24 ga Satumba, 2025 sojojin Operation Desert Sanity IV suka ƙwato wani adadi na fetur da taki da aka yi fasa-ƙaurin su. A yayin haka ne suka halaka ɗan leƙen asirin ƴan ta’adda da kama wasu mutane biyu da ke yi wa mayaƙan aiki.
A Adamawa, jami’in Bataliya ta 232 da sashe na 4 na jami’ai na musamman, sun yi nasarar ƙwato jarka 21 na fetur a Vintim, Tsamiya da Filin Ball da ke yankin Gella a Mubi.
Haka kuma, a rane 22 ga Satumbar ne hallau jami’an Bataliya ta 73 da ke aiki da CJTF da Hybrid Forces suka yi wa ƴan ta’adda kwantan-ɓauna a yankin Kolori Karumi da ke kusa da madatsar ruwa ta Alau a Borno, inda a nan ma suka halaka ɗan leƙen asirin Boko Haram yayin ba-takashi.
Kwana ɗaya bayan haka ne jami’an Task Force na Bataliya ta 112 suka kama ɗan shekara 54 mai suna Thomas James da ke ƙoƙarin safarar kwalabe 23 na fetur zuwa Gamboru-Ngala, wanda bincike ya nuna cewa yana aiki kai wa mayaƙan fetur ne.
Kazalika, a ranar 24 ga wata sojojin da ke aiki da ƴan sa kai suka kama mayaƙin Boko Haram mai suna Ahamdu Buba ɗan shekaru 31 a Garkida da ke Ƙaramar Hukumar Gombi a Adamawa. Ya ce ya shiga ƙungiyar ne tun a watan Afrilu, 2025 inda da shi aka kai wasu hare-hare ciki har da wanda ya yi sanadin lalata Gadar Mandahuma a farkon wannan shekarar.
