Ganduje ya caccaki Kwankwaso kan jita-jitar komawarsa APC

Spread the love

A ranar Alhamis ne tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da sauran jiga-jigan jam’iyyar na Kano suka gudanar da wani taro irinsa a karon farko a tsawon lokaci.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibril da sauran shugabannin jam’iyya na ƙananan hukumomi.

Abdullahi Ganduje ya ce sun shirya taron ne domin ƙara ɗinke jam’iyyar da yin kandagarki dangane da rigingimu ka iya taso mata a nan gaba.

Sai dai kuma majiyoyi na cewa an shirya taron ne da manufar yin kandagarki dangane da raɗe-raɗin da ake yi na komawar tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar ta APC.

To amma Abdullahi Gandije ya ce “mu ma mun ji wannan jita-jita ɗin kuma ba mu ɗauke muhimmiya ba. Mu a fahimtarmu da ƙuir’ar liman da ta ɓarawo a tsarin dimokraɗiyya duk ɗaya ne.”

Toshon gwamnan na jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shaida wa BBC cewa shi ba ya tunanin Rabi’u Musa Kwankwaso zai koma APC saboda wasu kalaman da Kwankwason ya yi a baya.

“Su yanzu abin nasu ya zamo wato ɗaukar ni amma ka da ka taɓa ni. Ya zama kamar an yi amai an lashe. Idan ka kula ya zazzagi Bola Tinubu lokacin da yake neman shugaban ƙasa. Sun ce Bola Tinubu kawai gina jihar Legas yake yi. Akwai lokacin da suka ce ma wai mahaukaci ne kawai zai shiga jam’iyyar APC.”

“Su suka ce sai mahaukaci ne zai shigo jam’iyyar APC. To ka ga yanzu tunda sun zama mahaukata suna son su shigo jam’iyyar sai mu hana su? Sai dai mu kira su da ƴan APC masu amai su lashe. Saboda haka muna yi musu marhaban su shigo jam’iyyar APC”, inji Ganduje kamar yadda BBCHausa ta ruwaito.

By Babaji