Mun sallami wasu ma’aikata ne don kauce wa zagon-ƙasa, inji Matatar Ɗangote

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar gudanarwar Matatar Ɗangote ta magantu akan rahotannin da ke cewa ta sallami ma’aikatanta, inda ta ce ta yi haka ne domin tseratar da kamfanin na biliyoyin daloli daga ayyukan zagon-ƙasa da ya fuskanta a baya.

Da fari, Ƙungiyar manyan ma’aikatan fetur da gas ta ƙasa (PENGASSAN), ta yi zargin cewa matatar ta sallami ma’aikatan da ke aiki a matatar da ɓangaren sinadaran mai ne jim-kaɗan bagan sun shiga cikin ƙungiyar, inda ta zargi hukumar gudanarwar da tauye ƴancin da dokar ƙasa ta ba su.

A sanarwar da Shugaban PENGASSAN, Abdulfatai Muhammed da Sakatarenta Eseoghene Choice suka fitar a jiya Juma’a, lamarin ya faru ne cikin sa’o’i 24 da ma’aikatan suka shiga ƙungiyar.

Haka kuma, ta yi zargin cewa an yi ta tsangwamarsu tun gabanin sallamar da aka yi musu inda ta je an janye motocinsu na zuwa aiki kafin abin ya faru, lamarin da ya sa suka biya har N4,000 domin zuwa ofis.

To saidai, duk da ikirarin ƙungiyar, matatar a wata takarda da ta fitar ranar Juma’a, ta musanta batun korar ma’aikata masu yawa daga aiki, amma ta ce tana da shirin yi wa tawagar ma’aikata garambawul sakamakon zargin ayyukan zagon-ƙasa a ɓangarorin kamfanin.

Ta kuma ce, matakin gyara da ta ɗauka abu ne da ke da muhimmanci musamman ganin yadda ya shafi al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, ta jaddada aniyarta ta cigaba da kula da ma’aikatanta da ƙoƙarin yi wa ƴan Nijeriya hidima da harkar makamashi a Nahiyar Afirka baki ɗaya.

By Babaji