
Rikici tsakanin Ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN da Matatar Ɗangote ya ƙazanta, lamarin da ya sa ƙungiyar ta bada umarni ga mambobinta da su tsunduma a yajin aiki a faɗin ƙasar.
Hakan zuwa ne kwanaki kaɗan da sallamar ma’aikata sama da 800 da ƙungiyar ta zargi Matatar ta Dangote a kai.
PENGASSAN ta bayyana cewa korar ɗimbin ma’aikata a kamfanin ba bisa ka’ida ba ne, wanda ya saba wa haƙƙin ƙwadago kuma ka iya zama babbar barazana a nan gaba.
A wata sanarwa, ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa kamfanin ya maye gurbin ma’aikatan da aka kora da Indiyawa sama da 2,000, lamarin da ta kira cin mutunci ga maiaikatan Nijeriya.
Akan haka ta ba da umarni a dakatar da duk wani aiki na isar da iskar gas da ɗanyen mai zuwa Matatar Dangote.
Sai dai, a martaninta, matatar ta musanta korar ma’aikata masu yawa, inda ta ce ta gudanar da sake fasalin cikin gida ne domin inganta aiki, kuma mafi yawan ma’aikatanta har yanzu ƴan Nijeriya ne.
Wannan rikici ya ƙara dagula alaƙar kamfanin da ƙungiyoyin ma’aikatan mai, musamman ganin cewa ƙungiyar NUPENG ma tana da saɓani da kamfanin kan haƙƙoƙin ma’aikata da tsaro.
PENGASSAN ta ce yajin aikin zai cigaba har sai an dawo da ma’aikatan da aka kora, tana mai kiran gwamnati, ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani.
