
Matan shugabannin ƙananan hukumomin jihar Adamawa guda 21 sun tafi Istanbul a ƙasar Turkiyya, domin shirin horarwa na mako guda da nufin koyon yadda za su tallafa wa mazajensu wajen shugabanci.
An ɗauki nauyin tafiyar ne da kuɗaɗen ƙananan hukumomin tare da shirin ƙungiyar ALGON, lamarin da tayar da ƙura a ciki da wajen jihar.
Haka kuma, masu suka sun ce kashe irin waɗannan kuɗaɗen a irin tsarin mulkin da aka kai, musamman ganin yadda jihar ke fama da talauci da rashin biyan albashi da kuma rashin isassun ababen more rayuwa.
Ajan hakan wasu ke kira ga hukumomin EFCC da ICPC su ƙaddamar da bincike akan lamarin.
Ra’ayoyin jama’a a shafikan sada zumunta sun nuna fushi, inda mutane ke ƙalubalantar dalilin tafiyar da kuma abinda ya sa aka je ƙasashen waje a maimakon yin ta a nan gida Nijeriya.
