Yadda ’yan gudun hijirar Borno suka gwammace zaman sansani fiye da koma wa gauruwansu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Watanni huɗu bayan da gwamnati ta kwashe sama da mutane 22,000 tare da wargaza hanyar samun ruwan su, sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke wajen birnin Maiduguri a yanzu ya sake zama kufai bayan yaƙin Boko Haram.

Sai dai Maryam Suleiman, mai shekara 50 bazawara ta ƙi fita.

Maryam da ’ya’yanta 12 na ci gaba da kwana a ƙarƙashin tsatsa, yayin da gine-ginen ke naman rugujewa.

“Sun ba mu zaɓi mu zauna ko mu koma gida,” inji ta, tana tsaye a cikin ragowar sansanin da iyalanta suka samu mafaka na tsawon shekaru goma. “Amma har yanzu Boko Haram na kashe mutane a can.”

Garin ta na Dongo da ke ƙaramar hukumar Mafa mai tazarar kilomita 49 daga Maiduguri ne mayaƙan Boko Haram suka kashe ƙannenta biyu a shekarar 2014. Haka kuma a nan ne gwamnati ta dage sai ta koma, inda ta ayyana yankin a matsayin “an samu lafiya.”

Amma duk da haka tabbacin gwamnati, Maryam ta dage ruɗu ne.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ba da umarnin rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira a shekarar 2023, saboda ingantacin tsaro da kuma buƙatar “dawo da martaba” ga mutanen da suka rasa matsugunansu.

Amma ya zuwa watan Mayun 2025, watanni bayan fara sake tsugunar da jama’a, mayaƙan Boko Haram sun ƙaddamar da sabbin hare-hare a Marte, inda suka kashe sojoji biyar a wani sansanin soji. An kai hare-hare makamantan haka a Dikwa, Rann, da Gajiram.

A cewar rahoton, sama da mutane 90 ne aka kashe a cikin watanni biyar da suka gabata a faɗin jihar Borno, inda harin Marte kaɗai ya tilastawa sabbin mazauna garin 20,000 yin gudun hijira.

“Na tuna a zamanin da al’ummarmu ke da albarkar noma,” Maryam ta tuna da hazaƙa ta mutanen Dango. “Mutanen Maiduguri sun yi tattaki zuwa yankinmu don yin kasuwanci, ban taɓa buƙatar ziyartar birnin ba, ina da duk abin da nake so a ƙauyenmu.”

Yanzu a kwarangwal ɗin sansanin Muna, Maryam tana ɗaki ɗaya da ‘ya’yanta 15, dukkan su babu mai zuwa makaranta.

“Da ƙyar mu ke cin abinci sai mun fita neman abinci,” inji ta. “Gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun cire komai lokacin da suka rufe sansanin.”

A ƙofar sansanin, Donoma Gamtayi, wani tsoho manomi daga garin Marte, yana kallon motocin sojoji suna bi ta kan garinsu.

“Har yanzu Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare,” inji shi a fusace. “Idan suka yi garkuwa da mutane, sai su nemi kuɗin fansa, wani lokacin har Naira miliyan biyu.”

“Idan aka tura jami’an tsaro a cikin al’ummominmu, za mu sami kwarin gwiwar komawa,” inji shi.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Kabir Adamu ya bayyana cewa, duk da cewa manufofin sake tsugunar da gwamnati na da nufin daidaita rayuwa, amma gaskiyar lamari na ci gaba da ɗaurewa.

“A wajen manyan garuruwan garrison, mutanen ƙauye har yanzu suna cikin mawuyacin hali,” inji shi. “Wasu ana tilastawa su biya kuɗin fansa ga mayaƙan Boko Haram ko ISWAP ayyuƙan da ke tallafawa ta’addanci a idon jihar, wanda ke nuna kama su.”

Wannan zagaye na tsoro, kwace, da azabtarwa ya bar ‘yan gudun hijira da yawa sun maƙale a tsakanin barazanar biyu: masu tayar da kayar baya da kuma doka.

Gwamna Zulum ya sha kare matakin rufe waɗannan sansanonin, yana mai cewa sansanonin sun zama matattara na “karuwanci, ‘yan daba, da cin zarafin yara.”

“Zama a sansanonin ‘yan gudun hijira ba shine abin da muka saba ba ko kuma abin da muke so a matsayinmu na mutane,” inji Zulum. “Mun yi imanin rayuwa mai aminci da mutunci hakki ne ga dukkan ‘yan Borno. Ba za a taɓa kawar da Boko Haram ba idan ba a sake tsugunar da su ba. Dole ne mutane su koma gidajensu su sami abin rayuwarsu.”

Sai dai hukumomin agaji sun ba da hoto daban-daban.

Asusun Kula Da ƙananan Yara Na Majalisar ɗinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargaɗin cewa, mutane miliyan 4.5 a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya na buƙatar agajin jinƙai, inda rabinsu ƙananan yara ne.

By ukarofi