Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a lokacin da tawagar yan majalisar dokokin Faransa da MSF ta Duniya ƙarkashin jagorancin Me Stephanie Doyin suka kawo masa ziyara a gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Ya sake nanata da jajircewar gwamnatinsa wajen yaƙar rashin abinci mai gina jiki da kuma matsalar rashin wadataccen abinci a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta tsara shirin raba abinci ga gidaje 120 masu rauni a kowace mazaɓa tare da tallafa wa yara 35,000 da aka sallama daga asibiti. Haka kuma ya umurci ma’aikatar lafiya da ta kafa cibiyoyin kula da abinci mai gina jiki a dukkan ƙananan hukumomi tare da ƙarfafa su bisa kyawawan tsare-tsare na MSF.
Dikko Raɗɗa ya kuma sanar da amincewar kafa masana’antar Tom Brown a Katsina, tare da shirin kafa babban kamfanin sarrafa abinci nan gaba.
Wakilan Faransa da tawagar MSF sun fara da ziyartar cibiyar Turai Yar’Adua, inda suka gana da ma’aikatan lafiya tare da duba irin ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu.
Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnati ta gano gidaje 120 masu rauni a kowace mazaɓa domin rabon abinci da yara 35,000 da aka sallama daga asibiti za su sami tallafin abinci na musamman.
Ya ce rashin tsaro a wasu sassan jihar ya durƙusar da kashe harkokin noma,wanda haka ya kawo ƙarancin abinci da taɓarɓarewar lafiyar yara.
“Abin da idona suka gani a wuraren da na ziyarta ya firgita ni matuƙa, kuma ya nuna mana dole mu ɗauki matakan gaggawa na haɗin gwiwa,” inji Malam Dikko.
Gwamna Radda ya jinjinawa ƙungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) kan ci gaba da aikinsu a jihar, inda ya ce rahoton MSF kan rashin abinci ba a ɗauke shi a matsayin suka ba, illa kuwa gargaɗi ne.
“Ya buɗe mana ido mun ga girman matsalar fiye da yadda muka zata. Nan da nan muka kafa kwamiti tare da MSF da sauran abokan hulɗa domin fito da shawarwari na gaggawa da na dogon lokaci,” in ji shi.
Gwamnan ya nanata cewa duk da cewa gwamnati ita ce ke da babban nauyi, haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na da matuƙar muhimmanci.
Mun ƙuduri aniyar samar da mafita mai ɗorewa, ya tabbatar a cewar gwamnan.
Gwamnan yayi fatan cewa da zarar zaman lafiya ya dawo a karkara, gonaki za su sake buɗewa manoma, wanda zai bayar da damar samun ingantaccen abinci mai ɗorewa.
A nasa jawabin yayin ziyarar, jagoran tafiyar Mr Stéphanie Doyon tare da wakilan Faransa sun yaba wa matakan gaggawa da gwamnatin jihar ta ɗauka, ciki har da rarraba abinci da yawa, samar da kayan gona, da kuma shirye-shiryen samar da zaman lafiya da ke baiwa manoma damar komawa gonakinsu.
Yan majalisar dokokin Faransa sun kuma yi alƙawarin taimakawa ƙoƙarin Katsina na yaƙar rashin abinci mai gina jiki da kuma ƙarfafa tsaron abinci.
