Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wani yunƙuri na rage zaman kashe wando da samar da hanyoyin dogaro da kai ga matasa, ofishin shugaban matasan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na Jihar Katsina ya gudanar da horon koyar da sana’o’i tare da yaye ɗalibai kusan 100 da suka fito daga sassan jihar.
Taron ya gudana ne a ofishin madugun adawar Jihar Katsina, Dr. Mustapha Muhammad Inuwa, inda shugabanni da mambobin jam’iyyar suka halarta don nuna goyon baya da yaba wannan ƙwazon matasa.
Da yake bayani kan maƙasudin horon, shugaban matasan jam’iyyar ADC na Jihar Katsina, Hon. Aliyu Umar wanda aka fi sani da “Sarkin Yaƙi”, ya bayyana cewa wannan horo na daga cikin muhimman ayyuka da jam’iyyar ADC ke aiwatarwa domin yaƙar zaman kashe wando da kuma farfaɗo da rayuwar matasa.
“ADC jam’iyya ce da ke fafutukar ganin matasa sun samu dogaro da kai ta hanyar koya musu sana’o’in da zai amfane su da al’umma,” inji shugaban matasan.
Ya ce wannan shiri zai ci gaba da gudana har sai lokacin da ADC ta karɓi mulki a matakin jiha da na ƙasa,” in ji Hon. Sarkin yaƙi.
Da yake jawabi a wajen taron,madugun adawa kuma tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha Inuwa, ya jinjinawa wannan namijin ƙoƙari na shugaban matasan ADC da sauran jagororin jam’iyyar wajen ɗaukar nauyin horar da matasa.
Ya bayyana wannan aiki a matsayin ginshiƙi mai ƙarfi na ciyar da jihar gaba.
“Ina taya shugaban matasan ADC murna bisa wannan aiki na alfanu, kuma muna fata irin wannan shiri zai ci gaba da samun goyon baya domin matasanmu su samu kyakkyawar makoma,” a cewarsa.
Dr. Mustapha ya kuma yi godiya ta musamman ga shugaban jam’iyyar ADC na jihar Katsina, Hon. Usman Musa Wamba, bisa yadda ya tsaya tsayin daka wajen ganin wannan shiri ya tabbata cikin nasara.
Ana sa ran waɗanda aka horas za su ci gaba da karɓar tallafi da goyon bayan jam’iyyar domin tabbatar da cewa abubuwan da suka koya sun amfane su da kuma zamantakewar al’umma baki ɗaya.
Kuma ana fatan wannan horo da matasan suka samu zai taimaka wajen rage bangar siyasa da yawaitar maula a wajen yan siyasa.
