Kwamitin da ya zaƙulo ma’aikatan bogi a ƙananan hukumomin Katsina zai ci gaba da aiki a matakin jiha

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta sake rantsar da kwamitin da ya yi aikin tantancewa tare da zaƙulo ma’aikatan ƙananan hukumomi na boge, a matsayin kwamitin da zai fara tantance ma’aikatan na matakin jiha.

Shugaban ma’aikata na Jihar Katsina Alhaji Falalu Bawale shine ya jagoranci rantsarwar a karo na biyu.

Ya bayyana cewa “ganin irin ƙoƙarin da kwamitin yayi a baya wajen tantancewa da kuma zaƙulo ma’aikatan boge a matakin ƙananan hukumomi yasa gwamnatin jihar ta sake ba su dama domin aiwatar da aikin a matakin jiha.

Shugaban ma’aikatan ya ƙara da cewa sake kafa wannan kwamiti ya biyo bayan buƙatar tabbatar da tsabtace tsarin ma’aikata a jihar, tare da tabbatar da cewa ana biyan albashi ne ga waɗanda suka cancanta.

Bawale ya buƙaci mambobin kwamitin da su gudanar da aikin da gaskiya, da kuma adalci, domin tabbatar da sahihancin bayanan ma’aikata a dukkanin sassan gwamnati.

Da yake mai da martani, Shugaban Kwamitin Alhaji Abdullahi Abubakar Gagare ya buƙaci haɗin kai da goyan baya daga dukkanin ma’aikatan na faɗin jihar Katsina.

Gagare wanda tsohon babban sakatare ne a ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare a jihar ya sha alwashin gudanar da aikin bisa gaskiya da riƙon amana kamar yadda suka gudanar a baya.

Kwamitin ya gano ma’aikatan bogi 3488 a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.

Haka kuma kwamitin ya gano yadda wani sakataren ilimi a ƙaramar hukumar Zango da ke amsar albashin ma’aikatan bogi guda 28 a duk wata.

By ukarofi