
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Fetur da Gas PENGASSAN, ta shirya janye yajin aikin gama-gari da ta shiga a bayan da Matatar Ɗangote ta amince da dawo da ma’aikatan da ta sallama.
Ministan Ƙwadago da Ɗaukar aiki, Dakta Muhammad Dingyaɗi ya sanar da yarjejeniyar haka a wata takarda biyo bayan zama na kwana biyu da aka yi da wakilan ɓangarorin biyu a Abuja, ranakun Litinin da Talata.
Zaman ya samu halartar Mai ba Shugaban ƙasa akan Harkar Tsaro, ministocin kuɗi, kasafi da shirya tattali da Ƙaramin Ministan Fetur da ƴan sandan farin kaya DSS, da kuma jagororin ƙwadago.
An shiga zaman ne bayan rikicin PENGASSAN da Ɗangote ya yi ƙamari wanda ya sa ƙungiyar ta PENGASSAN ta umarci mambobinta da su janye raba mai ga matatar.
A sanarwar Ministan, zaman da aka yi ya warware matsalolin da suka haddasa rikicin, wanda ya samo asali daga ƙoƙarin tauye ƴancin ma’aikata daga ɓangaren matatar.
A nan aka cimma yarjejeniya da ita (matatar) akan hukumar gudanarwarta za ta dawo da ma’aikatan da aka kora ba tare da sun yi wani asara daga haƙƙoƙin da suka cancanci samu ba.
Haka kuma, an yanke cewa babu wani ma’aikataci da ya shiga rikicin ɓangarorin biyu da matatar za ta hukunta.
Akan haka ne PENGASSAN ta amince da koma wa bakin aiki bayan janye yajin aikin da ta shiga kwanaki kaɗan da suka gabata, yayin da kuma dukkan ɓangarorin suka amince da kiyaye ababen da aka cimma yarjejeniyar akansu.
