Shugaban ƙaramar hukumar Gombe zai mayar da yara 1,000 makaranta

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana shirin mayar da yara 1,000 da ba sa zuwa makaranta kafin ƙarshen watan Oktoba na bana.

Ya ce za a yi musu rijista tare da samar da jakunkuna, littattafai da sauran kayan karatu domin inganta iliminsu da kuma sauƙaƙa wa iyaye nauyin da ke kan su.

Barista Sani ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar domin rarraba kayan makaranta ga ɗaruruwan yara a cikin ƙaramar hukumar, abin da ya kawo farin ciki da kwarin gwiwa ga iyaye da malamai.

Ya ce matakin zai taimaka wajen rage yawan yara sama da 700,000 da aka kiyasta ba sa zuwa makaranta a jihar Gombe, tare da bai wa ƙananan yara damar samun makoma mai kyau.

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma yi kira ga iyaye da al’umma su rungumi wannan shiri, su tabbatar da cewa dukkan ‘ya’yansu suna halartar makaranta akai-akai, ba tare da yawo a tituna ba.

By ukarofi