Ya kamata zaman lafiya da adalci su zama gadon Nijeriya, inji Jakadiya Fatima Paga

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Yayin da Najeriya ke murnar cikar ta shekaru 65 da samun ‘yancin kai, jakadiya Fatima M. Paga, wakiliyar UN Women ga gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ta yi kira da a mayar da zaman lafiya da adalci ginshiƙin rayuwa da gadon ƙasa.

A wani saƙo na musamman na ranar ƙasa, Jakadiya Paga ta ce akwai buƙatar shugabanni su tashi tsaye wajen fitar da manufofi masu ma’ana, domin sauya halin da al’umma ke ciki, musamman a Arewa maso Gabas inda ake fama da tsaro da bala’o’in yanayi.

“Na shaida da idona yadda mutane ke rasa muhallansu saboda hare-hare, ambaliya da fari.

Duk da haka, ba mu yi ƙasa a gwiwa ba. Muna sake ginawa, muna murmurewa da ƙarfin zuciya, muna riƙe da fata ga Najeriya,” in ji ta.

Ta ce lokaci ya yi da shugabanni su wuce magana, su tabbatar da cewa tsaro, adalci da zaman lafiya sun zama gaskiya a rayuwar talakawa.

Jakadiya Paga ta kuma yi kira da a zuba jari sosai wajen cimma manufofin cigaba na duniya (SDGs), musamman batutuwan da suka shafi zaman lafiya, ilimi, tsaftar ruwa, kare muhalli da bunƙasar tattalin arziki.

“Wannan ba kawai ajandar duniya ba ce. Waɗannan manufofi su ne igiyar rai ga miliyoyin ‘yan Najeriya,” ta jaddada.

A ƙarshe, ta yi kira da a haɗa ƙarfi da gwiwa wajen gina ƙasa mai ɗorewa. “Yayin da muke ɗaga tutar ƙasa, mu kuma ɗaga muryoyinmu domin zaman lafiya, domin adalci, domin Najeriya inda babu wanda aka bari a baya,” in ji ta.

By ukarofi