An buƙaci Gwamnatin Tarayya ta fifita karkara wajen sayan amfanin gona

Spread the love

Shugaban ƴan ɓangaren awo na kasuwar Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano, Alhaji Yahuza Ibrahim ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sayi kayan amfanin gona da manoma na yankunan karkara suka noma a daminar bana.

A wata sanarwa da Jami’ar Yada Labarai ta Karamar Hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, ta ce Yahuza Ibrahim ya yi kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da ita yayin wata ziyara da ta kai wa kasuwar.

Shugaban ƙungiyar da ake kira ma’auna a kasuwar ta Badume, ya ce duba da irin matsalolin da manoma, musamman monaman kayan abinci suke fuskanta, na karyewar farashin kayan abinci da kuma irin tsadar taki da suka fuskanta a lokacin noman, akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta fito da wani tsari na sayen abin da suka noma domin rage musu asarar da suke fuskanta a halin yanzu.

Ya ce, halin da manoman suke ciki a bana, shi ne riba ga mai saye faduwa kuma ga mai sayarwa, wato manoma ke nan, inda ya ci gaba da cewa dukkan manoma na kasa suna cikin wani mayuwacin hali, amma shigar gwamnati cikin lamarin shi ne zai karfafa musu gwiwa su ci gaba da rungumar noma.

Alhaji Yahuza Ibrahim ya ƙara da cewa, sayan kayan noma a yanzu zai taimaki manoma, kumar nan gaba zai taimaki masu saye, musamman talakawa wanda idan lokacin ya yi, sai gwamnati ta fito da wanda ta saya ta rinka sayar da shi a kan farashi mai rahusa, abin da ya ce hakan zai bunƙasa tattalin arzikin manoma, inda kuma ya ce, saukin da aka samu yanzu daga Allah ne, sai dai ya yaba wa Gwamnatin Tarayya dangane da matakin da ta dauka na karya farashin kayan abinci a kasar nan.

“Allah ne ya kawo sauki, abin da za mu ce ke nan, amma yana da ruwa da tsaki a labaran da muke samu na cewar gwamnati ta yi odar masara, waken suya, shinkafa da dawa.” In ji shi.

A nasa jawabin, Sarkin Noman Badume, Malam Usman Ahmad, ya ce manoma da sauran masu sana’ar sayar da kayan abinci sun shiga cikin damuwa saboda rashin masu sayen kayan da aka noma da kuma irin matsalar tsadar taki tare da yawaitar taki mara inganci da manoma suka rinka cin karo da shi a kasuwar damina ta bana, wanda haka ya sanya mafiya yawan nomana ba za su iya mayar da kudin da suka kashe ba ta fuskar abin da suka noma a bana.

Sarkin kasuwar Badume, Malam Isa Muhammad, wanda mai bai wa shugaban Karamar Hukumar Bichi shawara a kan harkokin Tara Kudin Shiga, ya yi magana a madadin sa, ya cedaga cikin abubuwan da suka haifar wa da manoma matsala a bana, sun hadar da; yin amfani da iri mara kyau da aka samar da kuma taki mara kyau da wasu ‘yan kasuwa suka rinka sayarwa ga manoma, inda ya bai wa gwamnati shawara da ta dauki matakan kawo karshen wadannan matsaloli.

“Muna kira ga gwamnati ta sa ido a kan wasu kungiyoyi da suke kawo iri, su ce a yi amfani da shi, kuma ta rika tantancewa domin kada a kawo wa al’umarta iri mara inganci”, inji shi.

Sauran waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu a kan wannan al’amari sun hadar da; manyan manoma da ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki wajen gina rayuwar al’uma, inda suka bayyana cewa akwai bukatar gwamnatocin jihohi da tarayya su fito da sababbin dabaru da za su taimaka wa manoma wajen inganta harkokin nomansu tare da bunkasa tattalin arziƙinsu.

By Babaji